Usman Alkali Baba: Tarihin sabon Mukaddashin Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya

Usman Alkali Baba

Asalin hoton, NPF

Bayanan hoto, Usman Alkali Baba ya maye gurbin Mohammed Adamu, wanda ya yi fiye da shekara biyu a kan mukamin.

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nada DIG Usman Alkali Baba a zaman sabon Mukaddashin Babban Sufeton 'yan sandan kasar.

Sabon sufeton ya maye gurbin Mohammed Abubakar Adamu, wanda shekarunsa na ritaya suka cika a farkon wannan shekarar.

Ministan harkokin 'yan sanda Maigari Dingyadi ya bayar da sanarwar ranar Talata.

Ranar 4 ga watan Fabrairu ne Shugaba Buhari ya tsawaita wa'adin Mohammed Adamu da wata uku kodayake wata biyu kawai ya yi .

Tarihin Usman Alkali Baba

An haifi DIG Usman Alkali Baba a garin Geidam na jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya ranar 1 ga watan Maris na 1963.

Ya kammala Digirinsa na farko a fannin Kimiyyar Siyasa a Jami'ar Bayero da ke Kano a 1985.

Kazalika ya yi Digiri na biyu a Jami'ar Maiduguri a kan Harkokin Mulki a 1997.

Ya shiga aikin dan sanda a 1988 kuma ya rike manyan mukamai a bangarori daban-daban.

Mukaman da ya rike sun hada da mataimakin babban sufeton 'yan sandan a kan harkokin kudi da mulki, mataimakin babban sufeton 'yan sandan a shiyya ta 5 da ke Benin, da shiyya ta 4 da ke Makurdi, da shiyya ta 7 da ke Abuja.

Haka kuma DIG Baba ya taba rike Kwamishinan 'yan sanda na Abuja da jihar Delta.

Kafinnadin nasa a matsayin sabon Mukaddashin Babban Sufeton 'yan sandan Najeriya, ya shugabanci sashen binciken masu aikata manyan laifuka wato Force Criminal Intelligence and Investigation Department (FCIID).

DIG Alkali mamba ne a Kwalejin Tsaro ta Kasa da kuma kungiyar manyan jami'an 'yan sanda ta duniya.

Yana da mata da 'ya'ya.