Usman Alkali Baba: Shugaba Buhari ya naɗa sabon shugaban ƴan sandan Najeriya

Asalin hoton, Nigeria Police
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya nada DIG Usman Alkali Baba a zaman sabon Mukaddashin Babban Sufeton 'yan Sandan kasar.
Sabon sufeton zai maye gurbin Muhammad Abubakar Adamu, wanda shekarunsa na ritaya suka cika a farkon wannan shekarar.
Kakakin fadar shugaban Najeriya Malam Garba Shehu ne ya tabbatar wa da BBC hakan.
Usman Alkali wanda aka haifa ranar 1 ga watan Maris na 1963, ya fito ne daga Jihar Yobe da ke arewa maso gabashin Najeriya.
Ya samu shaidar digiri na biyu a harkar mulki daga Jami'ar Maiduguri bayan ya yi na farko a fannin adabi daga Jami'ar Bayero ta Kano.
A ranar 4 ga watan Fabrairu ne Shugaba Buhari ya ƙara wa Mohammed Adamu wa'adin mulkinsa a matsayin shugaban ƴan sanda na tsawon wata uku, bayan cikar shekarun ritayarsa.
A yanzu ya ci wata biyu da ƴan kwanaki cikin wata ukun da aka ƙara masa ɗin.
Ƙara wa'adin mulkin nasa a wancan lokacin ya jawo ce-ce-ku-ce a tsakanin al'ummar ƙasar.











