Buhari ya tsawaita wa'adin Babban Sifeton 'yan sandan Najeriya

Asalin hoton, Nigeria Police Force
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya tsawaita wa'adin Babban Sifeton 'yan sandan kasar Mohammed Adamu.
Shugaba Buhari ya bayyana haka ne a sakon da masu taimaka masa kan harkokin watsa labarai suka fitar da yammacin Alhamis.
Ya tsawaita wa'adin Babban Sifeton 'yan sandan ne da wata uku.
Sakon ya ambato Ministan kula da harkokin 'yan sanda, Maigari Dingyadi yana bayyana hakan a fadar shugaban kasar da ke Abuja.
A ranar Litinin din da ta gabata ce Mr Adamu ya kamata ya yi ritaya daga aiki bayan da ya shafe shekaru 35 yana aiki kamar yadda tsarin aikin dan sanda ya tanada.







