'Yan sandan da aka sace a kusa da Zamfara sun kuɓuta

Asalin hoton, AFP
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce an yi nasarar kuɓutar da jami'anta tara da ake zargin an yi garkuwa da su.
A ranar 8 ga watan Nuwamba ne aka bayar da rahoton sace jami'an tsakanin Ƙanƙara da Sheme a jihar Katsina bayan harin da ƴan bindiga suka kai wa motar da suke ciki.
Cikin sanarwar da ta fitar ranar Juma'a, rundunar ta ce jami'an waɗanda dukkaninsu masu muƙamin ASP suna kan hanyarsu ne ta zuwa Gusau jihar Zamfara daga Maiduguri lokacin da abin ya faru.
Rundunar ta ce akwai jami'ai biyu da ke kwance a asibiti, yayin da sauran bakwai ke murmurewa.
Bayanan farko-farko
Bayanan da muka samu daga jihar Zamfara tun da farko a ranar Juma'a sun nuna cewa jami'an 'yan sandan sun kubuta.
Wasu majiyoyi sun shaida wa BBC cewa 'yan bindigar sun saki 'yan sanda biyar da suka sace bayan da takwas daga cikinsu da suka riga suka tsere.
Bayanai sun nuna cewa an kwantar da 'yan sandan biyar a wani asibiti da ke Gusau, babban birnin jihar Zamfara inda ake duba lafiyarsu.
Tun da farko majoyoyinmu sun tabbatar da cewa 'yan sanda 12 masu mukamin ASP 'yan bindigar suka sace a wani ƙauye da ke tsakanin jihohin Katsina da Zamfara.
Sai dai wasu manyan majiyoyi daga gwamnatin jihar ta Zamfara sun tabbatar wa BBC cewa wasu daga cikinsu sun tsere daga hannun masu garkuwa da mutanen inda suka bar biyar a hannunsu.
"Wani shugaban 'yan bindiga da ya sa aka sace su ne ya mika su [biyar] bisa fahimtar juna ba tare da an bayar da kudin fansa ba. Yanzu suna hannun Kwamishinan 'yan sanda na Zamfara," in ji wata majiyarmu.
Sai dai wata majiya ta daban ta ambato daya daga cikin 'yan sandan yana cewa sai da ya biya kudin fansa kafin a sake shi.
Waiwaye
A farkon makon nan ne wasu daga cikin iyalan 'yan sandan suka shaida wa BBC cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da mazajensu su a kan hanyarsu ta zuwa Zamfara daga jihar Borno domin gudanar da aiki na musamman.
Matar daya daga cikin 'yan sandan ta shaida mana cewa an sace su ne kusan mako biyu da suka gabata tana mai cewa ta kwana biyu ba ta ji ɗuriyar mijinta ba sai da ta je barikin 'yan sanda na jihar Borno ta samu labarin cewa an sace mazajen nasu. Ta ce an gaya mata cewa daga bisani biyu sun tsere daga hannu 'yan bindigar inda suka buga waya hedikwata cewa an tafi da sauran.
Ta kara da cewa ce bayan wani lokaci ta samu yin magana ta waya da maigidan nata amma a takaice inda ya bayyana mata halin da suke cikin a hannun masu garkuwa da su.
"A ranar Laraba ne ya bugo ya ce min sun shiga hannun masu garkuwa da mutane, ya ce don Allah a yi kokari a jinginar da gidansa a samu ko da naira miliyan daya ne a gaggauta idan ba haka ba za a samu matsala," in ji ta.
Ta ce tun daga ranar ba ta sake jin muryarsa ba amma wani a cikin jami'an 'yan sandan ya buga mata waya inda ya ce mata su gaggauta harhaɗa kuɗaɗen fansar tasu.
A cewarta: "Ya ce za a harhaɗa dubu ɗari takwas-takwas kowannensu, muna kokarin haɗawa - ga mu nan dai ba ma iya barci sai addu'ar Allah ya fitar mana da su lafiya."
Matar ta bayyana cewa mai ɗakin daya daga cikin 'yan sandan da ke hannun masu garkuwa da mutanen ta rasu ta bar ta bar masa 'yaya biyar da yanzu haka suna barikin 'yan sanda a jihar Borno.
"Ba zan iya ce maka ina da wani sauran bayani ba, mu dai ga shi nan muna cikin takaici, Allah ya fito mana da su lafiya, a yi mana kokari don Allah a fito mana da su, ga 'ya'ya nan ba wanda suka mallaki aikin kansu, addu'ar da muke yi shi ne Allah ya fito mana da mazajenmu," a cewar matar.
Satar mutane domin karbar kudin fansa ta zama ruwan dare a arewa maso yammacin Najeriya musamman a jihohin Zamfara da Katsina da Kaduna.
Hukumomi sun ce suna ɗaukar matakan kare al'umma daga waɗannan masu satar mutane amma mazauna yankunan sun ce har yanzu ba su gani a kasa ba.











