An yi jana'izar John Magufuli na Tanzania a mahaifarsa

An binne tsohon shugaban Tanzania Marigayi John Magufuli a kauyensu da ke Chato a kasar.

Magufuli ya mutu ne a ranar Larabar makon jiya bayan shafe kusan makonni uku ba a ganshi a bainar jama'a ba.

An yi taron addu'o'i kafin a binne gawar marigayin inda shugabar kasa Samia Suluhu Hassan ta jagoranci al'ummar kasar.

Marigayin ya mutu ne a ranar 17 ga watan Maris yana da shekara 61 a duniya .

Hukumomin kasar sun ce shugaban wanda yana daya daga cikin shugabannin Afrika fitattu da suka ƙi yarda da cutar korona ya mutu ne a dalilin matsalar zuciya.

An yi masa taron addu'oi a farkon makon nan a Dodoma, babban birnin kasar kuma tun bayan wannan lokaci ake rangadin bankwana da gawarsa a sassan kasar.

Gwamnati ta ayyana zaman makoki na kwanaki 21 domin alhinin mutuwarsa kuma ta dakatar da duk wasu ayyuka na gwamnati.