Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
CPAC: Trump ya ce ba zai kafa sabuwar jam'iyar siyasa ba
Donald Trump ya ce ba zai kafa jam'iyyar siyasa ta kashin kansa ba, kuma ya sanar da 'yan Republican cewa matakin zai raba kan 'yan jam'iyyar ne kuma ya rage ma ta karfi a zabuka masu zuwa.
Ya sanar da wannan matakin ne a wani taron siyasa da ya halarta a Jihar Florida, wanda wannan ne karon farko da ya yi jawabi a bainar jama'a tun bayan da Joe Biden ya kayar da shi a zaben shugaban kasa.
Ya kuma yi shagube cewa zai sake tsayawa takara a zaben 2024.
Mista Trump ya kuma soki Shugaba Biden, yana cewa ya mayar da Amurka daga matsayin farko zuwa matsayi na karshe.
Yawancin wadanda su ka halarci taron da aka fara tun ranar Alhamis sun kasance magoya bayan Mista Trump ne, kuma masu goyon bayan nasa kamar Ted Cruz, dan majalisar dattawa da dansa Donald Trump Jr na cikin wadanda su ka yi jawabi ga mahalarta taron.
An dai kori tsohon shugaban daga dandalin sada zumunta, ciki har da na Twitter da na Facebook saboda matakan da ya dauka na tunzura magoya bayansa su kai wa majalisar kasar at Amurka hari.
Tun bayan da aka kayar da shi, tsoho shugaban ya koma zama a wani gidansa da ke Mar-a-Lago a Jihar Florida.