CPAC: Trump ya ce ba zai kafa sabuwar jam'iyar siyasa ba

Donald Trump speaks at the Conservative Political Action Conference in Orlando, Florida, February 28, 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan ne karon farko da Donald Trump ya yi jawabi tun bayan da ya bar fadar White House

Donald Trump ya ce ba zai kafa jam'iyyar siyasa ta kashin kansa ba, kuma ya sanar da 'yan Republican cewa matakin zai raba kan 'yan jam'iyyar ne kuma ya rage ma ta karfi a zabuka masu zuwa.

Ya sanar da wannan matakin ne a wani taron siyasa da ya halarta a Jihar Florida, wanda wannan ne karon farko da ya yi jawabi a bainar jama'a tun bayan da Joe Biden ya kayar da shi a zaben shugaban kasa.

Ya kuma yi shagube cewa zai sake tsayawa takara a zaben 2024.

Mista Trump ya kuma soki Shugaba Biden, yana cewa ya mayar da Amurka daga matsayin farko zuwa matsayi na karshe.

Supporters hear Donald Trump speak at the Conservative Political Action Conference in Orlando, February 28, 2021

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wasu magoya bayan Mista Trump a wajen taron sun rika sowa suna yaba wa Mista Trump

Yawancin wadanda su ka halarci taron da aka fara tun ranar Alhamis sun kasance magoya bayan Mista Trump ne, kuma masu goyon bayan nasa kamar Ted Cruz, dan majalisar dattawa da dansa Donald Trump Jr na cikin wadanda su ka yi jawabi ga mahalarta taron.

An dai kori tsohon shugaban daga dandalin sada zumunta, ciki har da na Twitter da na Facebook saboda matakan da ya dauka na tunzura magoya bayansa su kai wa majalisar kasar at Amurka hari.

Tun bayan da aka kayar da shi, tsoho shugaban ya koma zama a wani gidansa da ke Mar-a-Lago a Jihar Florida.

A golden statue of Donald Trump is seen being moved into CPAC conference

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A wajen taron an rika sayar da kayayyaki, ciki har da wannan mutum-mutumin na tsohon shugaban