Saudiyya : Amurka ta sanyawa wasu jami'an ƙasar takunkumi saboda kisan Khashoggi

Gwamnatin Amurka ta sanar da sanya takunkumi kan dimbin 'yan Saudiyya bayan wani rahoton leken asiri da aka gano cewa Yarima Mai Jiran Gado Mohammed bin Salman ne ya amince da wani shiri na kamawa ko kashe dan jaridar da ke adawa da shi wato Jamal Khashoggi.

Matakan sun hada da hana biza da kwace kadarorinsu dake kasar Amurka

Sai dai babu wani mataki da aka sanar da dauka a kan shi Yarima mai jiran gado, da rahoton ya ce shine ya bada umarnin yin kisan.

Sakataren harkokin wajen na Amurka, Antony Blinken, ya ce matakan ba sa nufin lalata alakar Amurka da Saudiyya.

An kashe Mr Khashoggi tare da gididdiba namansa, a karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke Istanbul a cikin shekarar 2018.

Rahoton ya ce Yariman na ɗaukar Mista Khashoggi a matsayin barazana, inda ya goyi bayan a ɗauki ko da mummunan mataki ne domin rufe bakinsa.

Mista Biden na buƙatar masu kare haƙƙin bil adama da su taka muhimmiyar rawa a dangantakar da ke tsakanin Amurka da Saudiyya, kuma ɗaya daga cikin rawar ita ce fallasa wannan rahoton sirrin.

Washington ta kuma sanar da wata sabuwar manufar duniya da ta kira albarkacin Khashoggi, wadda za ta samar da kariya ga yan jarida yayin tsallaka iyakokin kasashe.