Yakin Yemen: Joe Biden na son Saudiyya ya kawo karshen yakin da ƴan Houthi

Amurka za ta kawo karshen goyon bayan da ta ke ba kawayenta da ke yaki a Yemen, kasar da aka daidaita da rikicin shekara shida wanda kuma ya lakume rayuka fiye da 110,000.

"Tilas a kawo ƙarshen yaƙin Yemen," inji shugaban Amurka cikin wani jawabi na alƙiblar da gwamnatinsa za ta fuskanta a fagen dangantakar ta da ƙasashen waje.

A karkashin shugabannin Amurka biyu na baya-bayan nan da ya gada, Amurka ta rika goya wa Saudiyya baya ne a yakin da ta ke yi da 'yan Houthi na Yemen.

Wannan rikicin ya janyo wa miliyoyin 'yan kasar ta Yemen wahalhalu da matsananciyar yunwa.

An dai fara yakin ne a 2014 tsakanin gwamnatin Yemen da kungiyar 'yan tawaye ta 'yan Houthi. Bayan shekara guda rikicin ya kara kazancewa bayan da Saudiyya da kawayenta - kasashen Larabawa takwas - da Amurka ke mara wa baya tare da Birtaniya da Faransa su ka fara kai wa 'yan Houthin hare-hare.

Amma Mista Biden ya sanar da sauyin alkibla a dangantakar Amurka da sauran kasashen duniya, wanda ya hada da wannan matakin na kawo karshen yakin

Kalaman Mista Biden sun yi hannun riga da na mutumin da ya gada - tsohon shugaba Donald Trump wanda ya sauka daga mukaminsa a watan jiya.