Wutar rikici kan birnin Marib na kasar Yemen ka iya haifar da barazana ga kai agajin jin-kai

    • Marubuci, Daga Paul Adams
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Wakilin Diflomasiyya

Birane biyu na kasar Yemen. Munanan hare-hare biyu. Tashe-tsahne hankula biyu.

Kana har yanzu akalla za a ce, sakamako biyu ne mabanbanta.

A tsakiyar shekarar 2018, dakarun da kasar Saudi Arabia da ke taimaka wa gwamnatin kasar Yemen da kasashen duniya suka san da zamanta sun kaddamar da shirin "Operation Golden Victory", da nufin kawar da mayaka 'yan tawayen Houthi daga yankin tashar ruwan Hudaydahmai muhimmanci da ke kan tekun Bahar Maliya mai muhimmanci.

Majalisar Dinkin Duniya da kungiyoyi bayar da agaji sun yi gargadin abkuwar mummunar matsalar da za ta shafi agajin jin-kai.

Kashi tamanin bisa dari na duka kayan agajin da ake shigowa da su kasar ta Yemen na bi ta cikin tashar jiragen ruwan.

Matsin lambar kasashen duniya sun haifar da tsagaita wutar da Majalisar Dinkin Duniya ke goyon baya. An kawo karshen artabun a watan Disamba, tare da hana ruwa gudu game da ba-ta-kashin.

Wannan karon,'yan tawayen Houthi ne ke kai farmaki a kan birnin mai matukar muhimmanci.

Marib shi ne kadai yankin da ya rage a karkashin ikon gwamnati a arewacin kasar Yemen.

Kuma shi ne babban birnin yankuna masu samar da man fetur na kasar.

Rasa birin na Marib na nufin wani babban koma baya ga gwamnatin da kuyma kasashen waje masu mara mata baya.

Ba kamar Hudaydah ba, muhimmancin birnin Marib a kasar ta Yemen abu ne da ba zai misaltu ba.

Wuri mai cike da turɓaya, da aka manta da shi kafin a fara yakin, Marib ya zama wani babban birnin mai cike da hada-hada, saboda isowar dubban 'yan kasar Yemen da suka rasa matsugunansu daga sauran sassan kasar.

Lokacin da na ziyarci birnin shekaru biyu da suka gabata, na samu mutane daga sassan kasar da dama, zaune a cikin sansanoni masu cike da datti da aka kafa a birnin mai tsohon tarihi.

An raba su da komai nasu. Duka suna da labarai game da gujewa yakin da kuma mayakan Houthi. Amma duk da haka sun samu tudun mun tsira.

Makonni biyu da suka gabata, fadan ya kara rincabewa, bayan da mayaka 'yan tawayen Houthis suka kaddamar da hare-hare daga kusurwoyi uku.

A halin yanzu birnin na cigaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali, duk da cewa mahukunta sun ce an harba makamai masu linzami a wajen birnin a ranar 7 ga watan Fabrairu , tare da hallaka mutane uku.

Amma kuma a wajen sansanonin, a kusa da inda ake fafatawa, an shiga fargaba.

Sama da shekara guda da ta wuce, mutane fiye da 140,000 ne suka rasa matsugunai saboda fadan a yammacin Marib, kamar yadda hukumar lura da masu kaura ta kasa da kasa Migration (IOM) ta bayyana.

Mutane fiye da 10,000 ne suka tsere a cikin makonni biyu da suka gabata kadai. Akasari sun nemi mafaka a kusa da birnin, tare da kara haddasa karin matsalolin samar da agaji da tuni ake fama da su.

"Muddin rikicin ya kara matsawa kusa da birnin da yankunan da kewaye da yankunan, hakan ka iya sa karin wasu mutane 385,000 rasa matsugunansu," hukumar ta IOM ta bayyana a wata mujallar da ta wallafa a baya-bayan nan.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi yunkuri da dama kan a dakatar da fadan, amma kuma har yanzu yunkurin kasa da kasar bai yi tasiri ba wajen nausawa da fadan zuwa birnin.

Ga wasu masu sa ido, abubuwan da suka faru shekara uku da suka gabata abin damuwa ne.

"Kasashen duniya sun yi amfani da karfin fada a jinsu kan kasashen Saudiyya da Yemen wajen dakatar da hare-hare a birnin na Hudaydah," in ji Nadwa al-Dawsari, wata malama cibiyar ilimi ta yankin Gabas ta Tsakiya a Washington.

"Amma kuma mayakan Houthi sun yi amfani da wannan damar wajen sake hadewa,'' ta ce.

"Kuma yanzu suna yin barazana ga birnin Marib."

Sabbin sauye-sauye na baya-bayan nan a manufofin gwamnatin Amurka, ta ce, bai taimaka ba.

Cikin makonni biyu da kama aiki, shugaba Joe iden ya sanar da kawo karshen goyon bayan da Amurka ke bayarwa wajen ayyukan soji da gamayyar dakarun Saudia a kasar ta Yemen, tare da janye batun ayyanawar da gwamnatin Trump ta yi wa 'yan tawayen Houthi a matsayin '' Kungiyar 'yan ta'addar kasa da kasa''(FTO).

A cikin kwanaki kadan mayakan na Houthi suka kara kaimi wajen hare-harensu.

"Hakan ya kara wa mayakan na Houthi karfin gwiwa," Nadwa al-Dawsari ta ce.

Dalilan janye batun ayyana ''Kungiyar 'yan ta'addar FTO na da karfi.

Kungiyoyin bayar da agaji sun ce, kamar yadda suka yi lokacin kai farmaki na gamayya a kan Hudaydah, yanayin kai kayan agaji ga kashi 70% na 'yan kasar ta Yemeni da ke zaune a yankunan da ke karkashin 'yan tawayen Houthi ka iya zama wani babban bala'i.

"Idan baka mayar da hankali ba game da samun damar kusantar mayakan na Houthi ba, za ka iya jefa kasar Yemen cikin karin wani tashin hankali," in ji Baraa Shiban, wani tsohon mai bai wa ofishin jakadancin Yemen shawara a London.

"Wannan ita ce babbar fargabar ga yadda gwamnatin Biden ta tunkari lamarin."

Daya abin fargabar shi ne har yanzu manufofin gwamnatin Amurka na mayar da hankali sosai kan damuwar yankin, ba wai ta hanyar yunkurin fahimtar shin da farko ma mai yasa kasar Yemen ta wargaje.

A bangaren Donald Trump, duka a kan kasar Iran.

Gwamnatinsa ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen bankado yadda kasar Iran ta ke mara wa 'yan tawayen Houthi baya, tare da nuna halin ko in kula kan yadda aka tafka asarar rayukan fararen hula da dakarun Amurka kawayen Saudi Arabia suka haddasa.

Yanzu kasar Saudiyya ce ta samu kanta cikin rashin samun wata madafa, yayin da gwamnatin Biden ke kokarin samun hanyoyin yin garanbawul ga yarjejeniyar nukiliyar Iran ta shekarar 2015, wacce Trump ya watsar.

"Tattaunawar da ba mu yi ba ita ce game da ita kanta kasar Yemen ," in ji Peter Salisbury, babban jami'in kungiyar masu sharhi kan rikicin

Ya yi amanna da matakin Mista Biden na nada kwararre dan kasar Yemen, Timothy Lenderking, a matsayin manzo na musamman ga Amurka a kasar ta Yeemen, amma kuma ya ce har yanzu gwamnatin bata yi cikakken bayanai game da sabbin manufofintsa

Mayar da hankali kan Marib, y ace, zai zama wuri mai kyau da ya kamata a fara da shi.

"Masu ruwa da tsaki kan abkuwar bala'oin da suka shafi jin kai na kasa da kasa, kamar yadda suka yi a Hudaydah," in ji sabon rahoton kungiyar sa ido kan rikicin kasa da kasa.

"Idan manyan kasashen duinya suka gaza daukar matakan dakatar da fadan yanzu, zai iya haifar da cikas ga irin matakan da aka dauka a baya, yayain da kasar ta Yemen ke kara fadawa cikin sabbin tashe-tashen hankula ba.