An ceto wasu ƙananan yara a gidan mata matsafa a Anambra

Asalin hoton, Nigeria Police Force
Rundunar 'yan sandan jihar Anambra da ke kudu maso gabashin Najeriya ta ce ta ceto wasu kananan yara uku a hannun wasu mata matsafa.
Sanarwar da rundunar ta fitar mai dauke da sa hannun kakakinta Haruna Mohammed ta ce an kama matan biyu - Mrs Chidi Felicia Nwafor, mai shekara 80 da Rejoice Raymond, mai shekara 39 inda ake zarginsu da laifin gallaza wa yaran uku da kuma daure su ba tare da izininsu ba.
"Ana zargin mutanen ne da killace kananan yaran uku (maza biyu da mace daya) a dakuna daban-daban a gida mai lamba 13 da ke kan titin Akunwanta Mbamalu, Federal Housing Estates 3-3 Nkwelle Ezunaka, sannan suka gallaza musu da azabtar da su ba tare da ciyar da su ba," a cewar sanarwar.
Wasu rahotanni sun nuna cewa matan biyu sun kama yaran ne da zummar yin tsafi da su, kuma rundunar 'yan sandan ta ce ta gano wasu kayayyakin yin tsafi da kuma bulala wadda ke da jini a jikinta da hade-haden magungunan gargajiya da makamantansu a dakunan da aka same su.
Rundunar ta ce ta ceto yaran daga gidan da aka samu matsafan kuma an garzaya da su asibiti domin duba lafiyarsu.
Kwamishinan 'yan sandan jihar Monday Bala Kuryas ya yi umarni a gudanar da bincike kan batun domin a tabbatar da yin adalci ga wadanda lamarin ya shafa, a cewar sanarwar.







