Zaɓen Nijar 2020: Muhimmancin zaɓen shugaban ƙasar Nijar ga Afirka

Zaɓen Nijar
    • Marubuci, Ishaq Khalid
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Hausa, Abuja, Nigeria

Zaben shugaban kasa da ake yi a Jamhuriyyar Nijar na da matukar muhimmanci ba ga kasar kawai ba, har ma a tsakanin kasa da kasa musamman a nahiyar Afirka.

Wannan shi ne karo na farko da a zahiri ake da kyakkyawan fatan sauya mulki cikin lumana daga zababben shugaban kasa zuwa wani zababben shugaban a tsarin dimokuradiyya tun da kasar ta samu mulkin kanta daga Turawan Faransa a 1960.

Duk wani yunkuri da aka yi a baya na sauya hannun mulki bisa tafarkin dimokuradiyya, ya gamu da cikas sakamakon juyin mulki na soja da kasar ta yi ta fuskanta.

Ana zaben zagaye na biyu ne yau Lahadi bayan da aka kasa samun dan-takara da ya yi nasara falan daya a zagayen farko da aka yi a wata Disamba - cikin 'yan takara 30 da suka fafata.

Yanzu 'yan-takara biyu da suka kasance kan gaba a zagayen na farko- wato Bazoum Mohamed na jam'iyyar PNDS Tarayya mai mulki da kuma Mohamane Ousmane na jam'iyyar RDR Tchandji ne ke neman maya gurbin shugaba Mohamadou Issoufou mai barin gado - wanda zai sauka bayan kammala wa'adin mulkinsa biyu da kundin tsarin mulkin kasar ya kayyade.

Kowanne cikin 'yan takarar biyu ya samu goyon bayan jam'iyyu da 'yan takara da dama wadanda suka fafata a zagayen na farko amma suka kasa zuwa zagaye na biyu. Amma dan-takarar jam'iyya mai mulki Malam Bazoum wanda tsohon ministan cikin gida na samun goyon bayan shugab mai barin gado Mohamadou Issoufou.

Shi kuma dan jam'iyyar hamayya Mohamane Ousmane wanda tsohon Firayim-Minista ne - yana samun goyon bayan dadadden madugun adawa Hama Amadou wanda Kotun Tsarin Mulki ta haramta masa yin takara saboda a 2017 wata kotu ta same shi da laifin safarar jarirai daga Najeriya.

Nijar mai yawan al'uma kimanin muliyan 23, tana daga cikin kasashe mafiya talauci a duniya a cewar alkaluman Majalisar Dinkin Duniya.

To amma a 'yan shekarun nan ta gano dimbin arzikin man fetur lamarin da ya kara sanya fata a zukatan talakawan kasar cewa za a yi amfani da arzikin yadda yakamata domin kyautata yanayin rayuwarsu.

Wannan baya ga dimbin arzikin makamashin Yuraniyom da albarkatun noma da kasar ke da su.

'Yan kasar da dama musamman matasa na fatan samun saukin matsalar rashin aikin yi.

Gagarumar matsalar tsaro

Zaben Nijar

Haka nan duk wanda ya zama shugaban kasar na gaba, zai tarar da manyan kalubale ta fuskar tsaro ciki har da tayar da kayar baya na Boko Haram a kudancin kasar kusa da iyakarta da Najeriya, da kuma ayyukan kuniyoyin tayar da kayar baya masu alaka da al-Queda da IS yammacin kasar kusa da iyaka da kasashen Burkina Faso da Mali.

Ko a ranar zaɓen ma, an kashe ma'aikatan hukumar zaɓe a yankin Tillaberi yayin da motarsu ta taka nakiya.

A 'yan watannin nan, an kashe daruruwan mutane - sojoji da farar hula - yayin da dubbai suka rasa muhallansu sanadiyyar hare-haren wadannan kungiyoyi. Misali a watan Janairu, wani hari a kauyuka cikin jihar Tillabery dake yammacin kasar sun yi sanadiyyar mutuwar farar hula fiye da 100- wanda aka yi imanin yana daya daga cikin hare-hare mafiya muni a tarihin kasar, ta fuskar hasarar rayuka.

Salon mulkin duk wanda ya lashe zaben wajen tunkarar lamuran tsaron na da matukar muhimmanci ba ga Nijar kadai ba, har ma da kasashe makwabtanta da al'umiminsu.

Haka nan kamun ludayin shugaban zai iya yin tasiri a yunkurin kasashen duniya na yaki da ayyukan ta'addanci yayin da a halin da ake ciki dubun-dubatan sojojin kasa da kasa ke fafatawa da kungiyoyin tayar da kayar baya a yankin Sahel, ciki har da sojojin Faransa kimanin 5,000.