Ana zaben shugaban kasa zagaye na biyu a Nijar

Bayanan sautiRahoton Ibrahim Isa

Yau Lahadi, al'ummar Jamhuriyar Nijar miliyan 7.5 ke tururuwa rumfunan zaɓe domin kaɗa ƙuri'a a zagaye na biyu na zaɓen shugaban ƙasar.

Ƴan takara biyu ne a zaɓen da Mohammmed Bazoum na jam`iyyar PNDS Tarayya mai mulki, da kuma Mahaman Ousman na babbar jam`iyyar hamayya ta RDR Tchanji.

A zagayen farko na zaɓen ɗan takara Mohammmed Bazoum na jam'iyya mai mulki ya samu kashi 39.3 yayin da tsohon shugaba Mahamane Ousmane yake da kashi 16.9 cikin ɗari.

Bazoum dai yana da goyon bayan ƴan takarar da suka zo na uku da na huɗu a zagayen farko na zaɓen, shi kuma Ousmane yana sa ran samun goyon baya daga gamayyar jam'iyyun hamayya 18.

Bangaren hamayyar ya yi tur da zargin maguɗin zaɓe sannan ya ce ba zai yadda da sakamakon zagaye na biyu ba matuƙar ta lura an tafka maguɗi.

Zabe a Nijar

Zaɓn na yau shi ne karon farko da za a miƙa da kuma karɓar mulki cikin lumana tsakanin shugabannin da aka zaɓa ƙarƙashin tsarin dimokraɗiyya a ƙasar da siyasarta ke tangal-tangal.

Nijar dai ta fuskanci juyin mulki sau huɗu a hannun Faransa cikin 1960. Ana sa ran samun sakamakon zaɓn na wucen gadi cikin kwanaki biyar.