Argentina : Wani minista ya yi murabus saboda zargin yin tsallaken layi a wajen yin rigakafin korona

Asalin hoton, Getty Images
Ministan Lafiya na Ajantina, Ginés González García, ya yi murabus bayan da aka zarge shi da taimaka wa wani dan jarida wajen yin tsallaken layi a wajen yin allurar rigakafin cutar koro
Dan jaridar mai shekara saba'in da daya Horacio Verbitsky, ya ce ya karbi kashi na farko na allurar rigakafin wanda Rasha ya samar, wato Sputnik Vee, a ginin ma'aikatar bayan ya yi magana da Mista González.
Ya bayyana shi a matsayin tsohon aboki.
Akwai karancin allurar riga-kafi a Ajantina kuma mutane kalilan ne daga cikin shekaru sama da saba'in aka yiwa rigakafi.
Mista González ya musanta tsoma baki a cikin ka'idojin bada fifikon
wajen yin allurar rigakafin, amma ya ce ya yarda, ya dauki cikakken alhakin gazawar sashen.na.
Gwamnati da masu adawa da ita na zargin juna kan ƙaruwar da ake samu ta masu cutar korona a ƙasar.
A ganin hukumomi, alhakin hakan yana kan masu karya dokoki ne.
Su kuwa masu suka a ganinsu gwamnatin ce ta gaza, tun da ba zai yiwu mutane su juri kasancewa cikin kaɗaici har tsawon watanni ba.










