Coronavirus a Argentina: "Mun gaji da zama a kulle tsawon wata biyar saboda annobar coronavirus"

A young woman walks in Buenos Aires in front of an outdoor poster asking people to stay at home

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, "Ku zauna a gida", abinda wani allon sanarwa ke fadam ke nan. Kawo yanzu Argentina ta ba da rahoron mutuwar mutane kalilan ne saboda corona, idan aka kwatanta da mafi yawan kasashe.
    • Marubuci, Veronica Smink
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Mundo, Buenos Aires

Wasu mutanen da ba a raba su da barkwanci a Ajantina sun ƙirƙiri wata kalma ''quareternal'', ma'ana ''kullen har abada'' suna danganta hakan da kullen da aka sanya saboda annobar cutar korona da ya ƙi ƙarewa.

Hakan na nuna yadda wasu ƴan ƙasar ke ji bayan da suke kasance cikin tsananin kulle na wata biyar - wani abu da ake ganin shi ne kullen annobar mafi tsawo da aka sanya a wata ƙasa a duniya.

Amma babu wanda ke yi wa tattalin arziƙin ƙasar da rashin mu'amala da juna da mummunan tasirin hakan dariya, waɗanda kullen ya shafa tun bayan sanya shi a ranar 20 ga watan Maris.

Dokar kullen ta fi shafar tattalin arzikin yankunan da suka kasance su ne zuciyar Ajantina kamar yankin cikin birnin Buenos Aires wato AMBA, inda kusan kashi 40 cikin 100 na al'ummar ƙasar ke rayuwa, sannan a can ne annobar cutar korona ta fi ƙamari da muni.

Ba a samu mace-mace sosai kamar wasu ƙasashe da dama ba

Zuwa ranar 25 ga watan Agusta, Ajantina ta samu mutum 350,000 da suka kamu da cutar korona - inda ta shiga jerin ƙasashe 15 da aka fi yawan masu cutar.

Amma zuwa yanzu mutum 7,300 kawai suka mutu, yawan da bai kai na maƙwabtan ƙasashe irin su Brazil da Chile da Colombia da kuma wasu ƙasashen yankin Turai ba.

A Italiya alal misali, duk da dokar kullen da aka sa ta kusan wata uku yawan waɗanda suka kamu da cutar na 260,298 bai kai na Ajantina ba, amma yawan waɗanda suka mutu a Italiyan ya haura 35,000.

Ana iya kwatanta Ajantina ne kawai da Philippines: ƙasar da ke yankin Asiya wacce ta sanya dokar taƙaita zirga-zirga ta wata huɗu, sannan ta samu yawan waɗanda suka kamu da cutar ƙasa da 200,000 da mace-mace 3,000 da ƴan kai.

Matakan ladabtarwa na Ajanatina suna da tsauri. Mazauna yankin AMBA ne kawai aka bai wa izinin fita yin sayayyar kayan abinci da sauran abubuwan buƙata.

Amma an haramta wa mutane fita shan iska

A priest gives a food parcel to a woman in a Buenos Aires church

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, 'Yan Argentina na fargabar cewa za su fuskanci matsalar tattalin arziki irin ta 2001-2002

Ma'aikatan da aikinsu ya zama tilas ne kawai ke da damar amfani da ababen hawa na haya ko kuma waɗanda aka ba su izini na musamman. Duk wanda ya fita da motarsa ba tare da takardar izini ba kuwa to zai iya rasa shaidarsa ta tuƙi.

Sai a kwanan nan aka bai wa mutane damar fita motsa jiki a wajen gidajensu. Tun a watan Yuni aka ba da damar fita motsa jikin amma ga mazauna babban birnin kawai kuma a wasu zaɓaɓɓun lokuta.

Mafi yawan waɗanda dokar taƙaita zirga-zirgar ta shafa yara ne: tun a watan Maris gwamnati ta bai wa yara mazauna yankin AMBA kaɗai izinin barin gidajensu don raka iyayensu yin sayayya

Rabuwar kawuna a siyasance

Hukumomin Ajantina sun ce waɗannan matakan sun taimaka wajen kare mutane da dama daga mutuwa sakamakon Covid-19.

Sun kuma bayyana cewa kashi 90 cikin 100 na masu cutar a Ajantina mazauna yankin AMBA ne.

A locked door painted with the Argentina flag

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Gwamnatin Argentina ta ce 90% na masu dauke da covid a kasar a yankin AMBA suke

A ƙiyasi, ana samun mace-mace 13.6 a cikin duk mutum 100,000 na ƴan ƙasar - wanda hakan bai kai na wasu ƙasashen na yankin Latin Amurka da dama ba da kuma sauran ƙasashen duniya.

Baya ga haka kuma, ƙasar ta yi ta ƙoƙarin kauce wa rushewar ɓangaren lafiyarta, duk da cewa yanzu haka babu isassun kayan aiki na fannin lafiya a wasu yankunan.

Haka kuma, mutane da dama na ganin an cimma abin da ake so na ainihin dalilin da ya sa aka sanya wannan doka ta kulle, kuma suna ganin ya kamata a ce an ɗage matakan tuntuni.

Mutane da dama tuni suka daina bin umarnin gwamnatin inda manyan tituna suka kasance cike da hada-hadar mutane a yanzu.

A wata ƙuri'ar jin ra'ayi da aka wallafa a ranar 3 ga watan Agusta a jaridar Pagina12, ta ce a yayin da mutum 8 cikin 10 na ƴan ƙasar suka ce dokar kullen ta yi nasara wajen rage yaɗuwar cutar, fiye da kashi 70 cikin 100 na mutanen kuwa sun nemi a sassauta dokokin ne, waɗanda a yanzu aka ƙara tsawaita su har zuwa ranar 30 ga watan Agusta.

A number of rosaries hang in the corner of a Bueno Aires hospital

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar yana karuwa, saboda watsi da dokar kulle da jama'a suka yi da kuma sassaucin da gwamnati ta yi

Bujirewa dokar kullen kuma a hannu guda ta janyo ƙaruwar waɗanda suka kamu da cutar. Yaɗuwar cutar na ƙaruwa a lokaci mafi muni; wato lokacin hunturu a kudancin duniya.

A yanzu haka dai, Ajantina na ɗaya daga cikin ƙasashen duniya da aka fi samun ƙarin masu kamuwa da cutar a duk cikin sa'a 24.

Zargin juna

Gwamnati da masu adawa da ita na zargin juna kan ƙaruwar da ake samu ta masu cutar.

A ganin hukumomi, alhakin hakan yana kan masu karya dokoki ne.

Su kuwa masu suka a ganinsu gwamnatin ce ta gaza, tun da ba zai yiwu mutane su juri kasancewa cikin kaɗaici har tsawon watanni ba.

A woman carrying an Argentina flag takes part in a protest in Buenos Aires

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Masu zanga-zanga sun yi machi a kan tituna domin adawa da matakin kulle da gwamnati ta sanya

Wata doka da gwamnatin ta sanya wa hannu a farkon watan Agusta ta haramta dukkan wasu taruka a gidajen mutane da kuma wuraren taro komai rashin yawan jama'a.

Karya wannan dokar na nufin aikata mummunan laifin da zai iya kai mutum gidan yari tsawon shekara biyu (duk da cewa dai zuwa yanzu babu wanda aka kama da laifin).

Dubban mutane sun yi maci a kan tituna a biranen ƙasar da dama ranar 17 ga Agusta don martani kan hakan. Su ne gagaruman zanga-zanga da Shugaba Alberto Fernandez ya gani tun hawansa mulki a watan Disamban bara.

Sai dai wasu da dama sun soki zanga-zangar, waɗanda suke ganin yin ta hatsari ne a yayin da annoba ke bazuwa.

Taɓarɓarewar tattalin arziki

Duk da cewa zai yi wahala a gane yadda tasirin cutar ta ragargaza tattalin arziƙin ƙasar sakamakon dokar kulle, gaskiyar magana ita ce Ajantina na fuskantar koma bayan tattalin arziki mafi girma tun bayan na shekarun 2001 zuwa 2002 da ta yi fama da ita.

Kafin annobar, dama ƙasar na cikin shekararta ta biyu kenan ta koma bayan tattalin arziki. A yanzu dokar kulle ta tursasa wa dubun-dubatar kasuwanci na fannonin da ba su zama wajibi ba kamar na saida kayan abinci rufe harkokinsu.

A family gathering for a barbecue

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, An haramta taruwar iyali domin shahararren bikin cin abinci na asados a lokacin kulle

Cibiyar Kasuwanci ta Ajantina ta ce fiye da ƙanana da matsakaitan ƴan kasuwa 42,000 ne suka rufe harkokinsu tun watan Maris, inda ya nunka sau biyu yawan waɗanda matsin tattalin arziki na 2001 zuwa 2001 ya shafa a ƙasar.

Yayin da ɗaruruwan ƴan Ajantina suka rasa kuɗaɗen shigarsu ko kuma ba su san ko za su samu aiki bayan dokar kullen ba, a hannu guda kuma ƙwararru na gargaɗi cewa za a fsukanci matsala a fannin lafiya.

Gidauniyar Ineco wadda wani fitaccen ɗan Ajantina masanin harkar lafiya Facundo Manes, ke tafiyar da ita ta gano cewa yawan masu matsalar damuwa ya ƙaru sau biyar, idan aka kwatanta da kafin lokacin annobar.

''Muna ganin wata annoba ta matsalar ƙwaƙwalwa,'' kamar yadda ƙwararren ya shaida wa wani gidan rediyo na Mitre.

''A farko lokacin da suke killace kansu, mutum shida cikin duk ƴan Ajantina 10 na fama da alamun damuwa mai tsanani ko saisa-saisa. Bayan kwanaki, alamun ba su kau ba amma sai lamarin ya dinga zama tsananin damuwa,'' in ji Manes.

"Idan muna samun mutane masu fama da ciwon damuwa, hakan na nufin muna fuskantar bala'in da ya shafi ɗan adam da tattalin arziki".

A flight schedule showing cancelled flights in Argentina

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Har yanzu jirage suna safara a ciki da wajen Argentina

Ƴan Ajantina da dama ba su san lokacin da 'za su yi tafiya ƙasashen waje ko 'ya'yansu za su koma makaranta ba.

An soke mafi yawan jiragen da ke zuwa ƙasar tsawon watanni kuma ma'aikatar sufurin jiragen sama ta riga ta sanar da cewa jirage ba za su koma zirga-zirga a ranar 1 ga Satumba ba kamar yadda aka tsara tun farko, wanda hakan ya sa Ajantina ta zamo cikin ƙasashe kaɗan da a yanzu haka babu zirga-zirgar jiragen sama a duniya.

Amma mai yiwuwa abu mafi jawo ce-ce-ku-ce kan wannan dokar kulle mai tsawo shi ne abin da ƙwararru a harkar lafiya suka kira "ana kukan targaɗe sai ga karaya ta samu."

Akwai damuwa cewa a yayin da dokokin suka yi aiki wajen daƙile yaɗuwar cutar korona, to za su iya jawo wasu matsalolin lafiyar kuma.

A group of mothers walks with their kids

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kamar sauran kasashe, annonbar ta shafi matan Argentina

Wani rahoto da Jami'ar of Buenos Aires (UBA) ta fitar ya ce fiye da rabin al'ummar ba su yi wani aiki da zai taimaka wa lafiyarsu ba tun da kullen ya fara.

Shida cikin mutum 10 sun ƙara ƙiba, a cewar ƙungiyar Argentine Nutrition Society (SAN), a cikin al'ummar da kashi 60 cikin 100 na mutanenta dama can ƙiba ta yi musu yawa.

Wasu daga cikin manyan cibiyoyin lafiya na ƙasar sun nuna damuwa kan yadda ake samun raguwar masu zuwa duba lafiyarsu asibiti tun fara dokar kullen.

Tsoron kamuwa da cutar korona ya rage yawan amfani da motocin haya da soke ganin likita, sannan dokar killace kai na daga cikin manyan dalilan da aka ba da misalansu na dalilin da ya sa dubban ƴan Ajantina ba su ga likita ba tun watan Maris.