Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Muhawara ta kaure tsakanin ƴan shekarun 1980s da matasa da ƴan bana-bakwai a Twitter a Najeriya
A baya-bayan nan, kalamai kamar Millennials, Baby-boomers, Gen Z da Gen X sun karaɗe shafukan sada zumunta musamman ma shafin Twitter.
Wannan rabe-rabe ne na mutane da suka danganci shekarun haihuwarsu kamar haka:
- Baby-boomers: mutanen da aka haifa tsakanin shekarun 1946 zuwa 1964
- Gen X: mutanen da aka haifa tsakanin shekarun 1966 zuwa 1980
- Millenials ko Gen Y: waɗanda aka haifa tsakanin shekarun 1980 zuwa 1995
- Gen Z: mutanen da aka haifa tsakanin shekarun 1996 ko 1998 ko 2000 zuwa yanzu
Ƴan ƙasa da shekara 25, wato ƴan Gen Z ba sa so ana sa su a jerin ƴan shekara 40 wato ƴan millenials kuma suna yawan bayyana hakan a shafukan sada zumunta musamman Twitter da TikTok.
Asali ma, wasu ƴan Gen Z cewa suke yi an kirkiri waɗannan shafuka ne don su, musamman ma shafin TikTok.
Sannan su kan yi shaguɓe ga ƴan Millennials su ce shafin Facebook ne dai-dai da su kuma shi kaɗai suke iya amfani da shi.
Ɓangarorin biyu kan zolayi juna ne bisa wasu halaye da suke zargin juna da su. Misali: ƴan millennials kan ce ƴan Gen Z shagwaɓaɓɓu ne, wato sun samu komai a ɓagas saboda sun zo a zamanin da aka samu ci gaba sosai a fannin kimiyya da fasaha.
Don haka akwai abubuwan da ba su san zafinsu ba kamar wahalar da aka sha a baya ta kiran waya da wayar tarho ta girke a gida, da bin layi a banki ba don amsar kuɗi tunda yanzu akwai na'urorin ATM a ko ina da dai sauransu.
Wato dai ƴan Gen Z sun buɗi ido da kimiyya fiye da ko wane rukuni na mutuna a duniya.
Haka kuma, yan Millenials na zargin ƴan Gen Z da zama masu bijire wa dokoki da tsananin son cin gashin kansu, kuma ba su da girmama na gaba ciki har da iyayensu.
Abin da suka fi saka wa a gaba kwalliya da ado da ƙyale-ƙyale.
A ɗaya ɓangaren kuma, ƴan Gen Z na zolayar ƴan millennials da cewa sun fara tsufa kuma ba su da wayewar kai kamar su.
Su kan ce millennials ƴan wahala ne da idonsu ya rufe da neman kudi sannan salon yadda suke ado bai da tsari.
Sai dai su millenials na cewa, ba wahala ba ce illa dai sun san ciwon kansu kuma iyayensu sun yi masu horo mai tsauri ta iya dogaro da kai.
Haka kuma, su kan ce ba su dogara da kimiyya da shafukan sada zumunta ba wajen gudanar da komai.
To, irin wannan muhawarar ce ta kaure a shafin Twitter a Najeriya tsakanin ɓangarorin nan biyu kuma masu amfani da shafin na ɓangarorin biyu na ta yada wa juna magana kuma kawo yanzu an yi amfani da maudu'in #Millennials da #GenZ fiye da sau 180,000.
An fara muhawarar barkwancin ne tsakanin rukunin mutanen biyu kuma sun ci gaba da zolayar juna kamar yadda suka saba.
Sun yi amfani da hotuna da bidiyo da ake kira 'meme' da 'gifs' wajen aika saƙonnin.
Wani mai amfani da shafin Twitter mai suna Bossbaeby ya rubuta:
"Ƴan millennials kan ce abin da babba ya hango a zaune ko yaro ya hau Rimi ba zai gan shi ba. Mu kuwa ƴan Gen Z sai mu ce abin da babba ya hango a zaune, ma yi amfani da jirgi marar matuki mu hango."
Wannan tweet dai ya nuna alfahari da ƴan Gen Z ke yi da iliminsu da ƙwarewarsu wajen amfani da kimiyya.
Shi kuwa TimiFash mai amfani da shafin na Twitter ya wallafa wannan sakon ne yana cewa: "Ƴan millenials a hanyarsu ta zuwa aiki da karfe 7:30 na safe bayan yin baccin awa uku da minti 26" sannan ya ɗora bidiyon wani mutum yana tuƙi a mota yana zargin kansa da zama wawa saboda ya bari ya makara wajen zuwa aiki.
Wannan saƙon dai ya bayyana kallon da yan Gen Z su ke yi wa ƴan millenials na wahalallu waɗanda ba su da wani jin dadi a rayuwa sai zuwa aiki da neman kuɗi.
Mai amfani da shafin Twitter Jaysonrogue ya wallafa wani saƙo da hotuna yana nuna bambancin yadda ƴan millennials da ƴan Gen Z ke mu'amala da juna. Yayin da ƴan millennials ke haɗuwa su yi hira su tattauna a tsakaninsu, ƴan Gen Z kuwa sai dai su yi ta danna wayoyinsu.
Wannan muhawarar dai na nan tana ci gaba a shafin Twitter a Najeriya, ɓangarorin biyu na ta zolayar juna.
Sai dai yayin da ake ta tafka wannan muhawara tsakanin millennials da Gen Z, wani bangare na nan yana tasowa wato wanda suke biyo bayan Gen Z. Su kuma ana kiransu Genration Alpha.