Twitter da Facebook sun dakatar da shafukan Shugaba Trump

Lokacin karatu: Minti 1

An dakatar da Donald Trump daga aika saƙonni a Twitter da Facebook bayan saƙon da ya aika wa magoya bayansa da suka kai hari ginin majalisar dokokin Amurka.

A wani saƙo da ya wallafa a shafukansa na sada zumunta zuwa masu zanga-zangar, ya ce, "Ina son ku" kafin daga bisani ya ce su koma gidajensu. Kuma ya maimaita ikirarinsa na bogi kan maguɗin zabe.

Kamfanin Twitter ya ce ya nemi a cire saƙonni uku da ya aika saboda "haɗarin da suke da shi wajen janyo koma baya ga zaman lafiyar fararen hular kasarmu".

Kamfanin ya ce shafin shugaban ƙasar zai ci gaba da kasancewa a rufe saboda zaman lafiya idan bai goge saƙonnin ba.

Ya kuma ƙara da cewa ci gaba da karya wasu ƙa'idojin zai iya kai wa ga rufe shafin @realDonaldTrump har abada.

A gefe ɗaya kuma, Facebook ya toshe sahfin Trump na awa 24. Sai Youtube da ya cire bidiyon da ya wallafa.

Facebook ya ce: "Mun cire ne saboda munyi amannar zai iya ƙara rura wutar rikicin da ake fama da shi a yanzu."

Magoya bayansa sun kutsa kai cikin ginin majalisar dokokin kasar tare da yin taho mu gama da 'yan sanda, wanda hakan ya janyo mutuwar wata mata.