Lafiya Zinariya: Shawarwari game da abincin da mata masu ciki ya kamata su ci
Latsa hoton da ke sama domin sauraren cikakken shirin Lafiya Zinariya:
Mata masu ciki a fadin duniya, na samun shawarwari kan abubuwan da ya kamata su ci, ko kuma wadanda ya dace su kauracewa.
Sai dai a wasu lokutan wadannan shawarwari na zuwa musu ne ta hanyar al'adu ko kuma wani lamari mai kama da canki-in-canka.
Wasu daga cikin camfe-camfen da ke tattare da hana masu juna biyu cin wasu nau'ukan abinci sun samo asali tun zamanin kaka da kakanni.
Ga misali a wasu yankunan karkara a Najeriya sun yarda cewa cin dodonkodi kan sa mace ta haifi yaro mara kazar-kazar.
Su kuma mata a kasar Japan ana gaya musu cewa cin yaji na sa yaro ya zama mai saurin fushi.
A Amurka idan an haifi yaro da tabo sai ace uwar ta yi kwadayin dan iccen nan strawberry ko kuma shambo lokacin da ta ke da ciki.
Can kuwa a kasar Mexico suna da wani dadadden camfi na cewa, cin kwai na sa a haifi yaro yana wari.
Abincin wani guban wani, kamar yadda masu iya magana kan ce, domin can a kasar philippines ana sa mai ciki ne ta sha danyen kwai gab da fara nakuda, saboda samun saukin haihuwa.
Su kuma al'ummar kasar Sin wato China al'adunsu na cike da abubuwa da dama da aka hana mai ciki ci. Ga misali cin kaguwa na sa yaro ya zama maketaci ko a haife shi da cindo.
Shan madara kuma na sa fatar jiki ta yi fari.
Yayin da cin wata dabbar teku da ake kira squid a turance, kan janyo mahaifa ta yi danko.
A jihar Andhra Pradesh da ke kasar Indiya ana gaya wa mata masu juna biyu cewa, gwanda da kabewa na da zafi ga jariri. Yayin da a wani bangare na jihar Gujarat kuwa duk wani farin abinci da suka hada da madara da kindirmo ko yogurt da ayaba ana hana matan ci, domin su kuma suna da sanyi.
A kasar Mexico suma suna da irin wannan camfin na sanyi ko kuma kayan abinci mai sa zafi.
Abin da ke sa ana hana mata da dama cin wasu kayan abinci da suka hada da kwai da tumaturi da kuma avocado.
A wasu yankuna na kasar Tanzania, ana hana mata cin nama, saboda tsoron kada jariri ya biyo halin dabbar da aka ci.
Haka kuma a wasu sassa daban-daban na nahiyar, ana hana mata masu juna biyu cin kwai, saboda yarda da cewa yana janyo rashin haihuwa.
Sai dai akwai wadanda ke ganin wasu daga cikin wadannan al'adu na kaka da kakanni sun fara bacewa.
A takaice a wasu bangarori na yankunan Afrika da Asiya da kuma Latin Amerika camfe-camfen kan hana mata masu juna biyu cin abinci mai gina jiki, ta hanyar barin wasu muhimman abubuwa da jiki ke bukata.
A likitance
Hukumar lafiya ta Burtaniya ta bayar da wasu shawarwari ga mata masu juna biyu kamar haka.
*-mata masu ciki su ci kayan marmari da ganyayyaki sosai, kamar sau biyar a rana.
*Su kuma ci abinci mai dauke da sinadarin Protein wato mai gina jiki da suka hada da nama da kifi da kwai da dangogin gyada.
*Haka ma abinci mai dauke da sinadarin Calcium kamar su madara da kindirmo ko yogurt.
*Yana da kyau kuma su ci kifi mai maiko kamar su mackerel da sardines, amma su guji cin kifayen da suka hada da shark da swordfish.
*Sannan yana da kyau su guji cin wasu nau'in cukwi da suka hada da Brie da Camembert da Gorgonzola da kuma Roquefort.
*Abubuwan kuma da kwata-kwata kuma bai kamata mai ciki ta ci su ba, a cewar hukumar sun hada da danyen nama da danyen kwai da danyen shellfish, da kuma duk wani nau'in fate.











