ISWAP ta yi wa sojojin Najeriya kwanton ɓauna a Borno

Aƙalla sojojin Najeriya uku rahotanni suka ce mayaƙan ISWAP sun kashe a wani harin kwanton ɓauna a Borno.

Wata majiyar sojin Najeriya ta tabbatar wa kamfanin dillacin labarai na AFP da kai harin, inda ta ce akwai sojoji biyu da suka ɓata a harin da aka kai da yammacin Juma'a.

Majiyar ta ce mayaƙan ISWAP sun buɗe wa ayarin sojin Najeriya wuta ne a ƙauyen Barwanti da ke yankin Tafkin Chadi bayan ɗaya daga cikin motar ayarin na sojojin ta taka nakiya da ƴan bindigar suka dasa.

An kai wa ayarin sojin na Najeriya hari ne yayin da suke kan hanyar zuwa Baga.

ISWAP da Boko Haram na ci gaba da zama barazana a yankin arewa maso gabashin Najeriya, inda suka kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da gidajensu.