Yadda korona ta gurgunta ayyukan sufuri a Najeriya
Ƙungiyar masu motocin sufuri ta Najeriya, wato NARTO ta koka game da matsalolin da sashen sufuri ke fuskanta a yanayin da ake ciki na cutar korona a duniya.
To sai dai kuma duk da hakan kungiyar na duba hanyoyin shawo kan matsalolin tare da faɗaɗa ayyukanta wajen samar da motoci a yankunan karkara domin kawo saukin sufuri ga mazauna yankunan karkara a ƙasar.
Yusuf Lawal shi ne sabon shugaban ƙungiyar ta NARTO kuma ya shaida wa BBC cewa ƙa'idar ba da tazara saboda kare yaɗuwar korona ya janyo koma-baya sosai a sana'arsu saboda direbobi ba sa samun yadda suke so - "ba sa samun juyawa ko a ɗauki kaya a sauke, ko a ɗauki mutane a mota sai an bar tazara".
Ya ce yin hakan yana shafar kuɗaɗen shigar direbobin sai dai ya yi fatan cewa nan gaba a samu sauki ta yadda direbobin za su dara.
A cewarsa, irin matsalolin da suke fuskanta da suka haɗa da matsalar rashin hanya mai kyau ga masu dakon mai "ba ma iya aiki da daddare saboda ɓarayi da masu sace mutane a kan hanya".
Wata matsalar da direbobin ke fuskanta a cewar Yusuf Lawal ita ce rashin tsaro "sai ka ga mutum ya ɗauko taki daga Legas kafin ya zo Kaduna an samu shingen bincike wajen 10".
Ya ce za su zauna da shugabanni tsaro domin tattaunawa kan yadda za a shawo kan matsalolin da suke fuskanta.







