Abin da ya sa jihohin kudu maso gabashin Najeriya suka haramta kiwo barkatai a yankunansu

Gwamnonin yankin Kudu Maso Gabashin Najeriya sun haramta yin kiwo barkatai, kamar yadda shugaban ƙungiyar gwamnonin yankin David Umahi ya ce.

Gwamna Umahi na Jihar Ebonyi ya ce yankin kudu maso gabashin ƙasar ya hana kiwon shanu barkatai a yankunansu.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin wani taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC da aka yi a Abakaliki babban birnin jihar ta Ebonyi.

Ƙungiyar gwamnonin Kudu Maso Gabas ɗin ta kuma haramta zirga-zirgar da makiyaya ke yi da shanu da ƙafa barkatai, sannan suka roƙi shugabannin makiyayan da su bi wannan doka a matsayinsu na ƴan ƙasa na gari don wanzar da zaman lafiya da haɗin kai.

Gwamna David Umahi ya ce: "Muna cikin wani mummunan lokaci, idan babu kishin ƙasarmu Najeriya a ranmu, zai yi wahala a samu zaman lafiya.

"Ya kamata shugabanni da masu ruwa da tsaki na wannan yankin su magantu su kuma daina sanya siyasa a cikin tsaron yankin da na ƙasar baki ɗaya.

"Gwamnonin Kudu Maso Gabas sun yi kira ga shugabanninmu da su yi magana a kan tsaron yankin da kuma haɗin kan Najeriya. Na karanta a jarida inda wani ya ce ya bai wa gwamnonin Kudu Maso Gabas kwana bakwai da su haramta kiwon barkatai.

"Gwamnonin Kudu Maso Gabas sun haramta kiwo barkatai da zirga-zirgar makiyaya da shanunsu da ƙafa a yankin, za mu kula da kanmu sosai, abin da muka tattauna da makiyayan abu ne da yake kan tsari tsawon lokaci."

Ya kuma yi gargaɗi ga mutanen yankin da su guji ingiza rikici a Najeriya ta hanyar yaɗa bidiyon ƙarya da ke iƙirarin mambobin ƙungiyar ƴan aware ta IPOB sun kashe Fulani a yankin Kudu Maso Gabas.

"Ya zama dole mutane su san cewa ba a siyasantar da tsaro, abin da suke tsammani daga shugabannin shi ne su yi wasu tsare-tsare da zai amfani al'umma ya kuma haɗa ƴan ƙasa."

Gwamna Umahi ya ƙara da cewa yana goyon bayan gano masu tayar da zaune tsaye daga dazukan ƙasar da koro su don samar wa ƙasar tsaro.

"A cikin dazukanmu a yau, akwai masu satar mutane don kuɗn fansa da makoyaya da matsafa da duk wasu masu aikata munanan maifuka, duk wani wanda ya samu kansa a daji to ya yi kasada, idan muka ce a zaƙulo mutane daga cikin dazukan, to don tsaronsu da zaman lafiyarsu ne, don haka ina goyon bayan zaƙulo duk wani mutum da ke cikin dazukanmu."

Wannan yunƙuri na gwamnonin Kudu Maso Gabshin Najeriya ya zo ne a daidai lokacin wasu jihohin Kudu Maso Yammacin ƙasar suke fuskantar ƙalubale na rikicin makiyaya.