Ghana: An kama wasu ma'aikatan lafiya da sayar da jarirai

Asalin hoton, Getty Images
An kama ƴan wata ƙungiyar masu "sayar da jarirai" da safarar yara a Ghana.
Wannan ya biyo bayan wani bincike na ƙarkashin ƙasa da aka gudanar inda aka sayar wa wasu masu bincike jarirai biyu kan dala 5,000 da dala 4,800.
Mutanen 11 da ake zargi sun haɗa da likitoci biyu da malaman jinya huɗu da iyaye mata biyu da ma'aikatan jin-ƙai biyu da ungozoma ɗaya.
Ana zargin suna gudanar da ayyukansu ne a asibitoci a Accra, babban birnin Ghana da birnin Tema mai maƙwabtaka.
Hukumomi na ganin cewa mai yiwuwa an shaida wa wasu daga cikin iyayen mata jariransu sun rasu ne bayan haihuwa.
Sun ce wasu matan masu ƙaramin ƙarfi kuma an ba su shawarar sayar da jariran ne.
A halin yanzu, jariran biyu da aka ceto na ƙarƙashin kulawar hukumomi.
Wakilin BBC a Accra, Thomas Naadi ya ce lamarin ya zo da mamaki a Ghana inda batun sayar da jarirai ba sabon abu ba ne amma ba a taɓa samun hujjar ana aiwatarwa ba.
A wasu ƙasashen a nahiyar Afrika, an sha gano gidajen sayar da jarirai a baya-bayan nan a Najeriya da Kenya, inda gwamnati ta ƙaddamar da bincike bayan BBC ta fitar da nata binciken.
An kwashe watanni ana binciken da ya haifar da kama mutanen a wannan makon a Ghana, kuma Kungiyar Likitoci da Ofishin Tattalin Arziƙi da Manyan Laifuka ne suka jagoranci binciken.
A bara ne wani direban tasi ya fara tsegunta masu lamarin.
An ƙwace lasisin likitocin biyu da aka kama har sai an gama shari'a a kotu.












