Binciken BBC Africa Eye ya gano yadda wasu mata ke sayar da ƴaƴansu tsabar talauci

Bayanan bidiyo, Binciken BBC Africa Eye ya gano yadda wasu matan ke sayar da 'ya'yansu tsabar talauci.

Latsa hoton sama domin kallon bidiyon

Wannan labarin wata uwa da ta faɗa tarkon talauci da masu fataucin kananan yara.

Klenice na fatan cewa ta hanyar ba da labarinta, sauran mutane za su yi karatun ta-natsu kafin sayar da ƴayansu saboda tsabar talauci.

Matsananciyar rayuwar da wasu ke ciki ta tilasta masu kasuwancin yara a ɓoye a Kenya wasu kuma saboda haɗamarsu.

Wasu daga cikin yaran na sata ne, wasu kuwa iyayensu mata ke sayar da su da gangan.

Binciken BBC Africa Eye na fasaƙwaurin yara, ya ta da hankalin mutanen Kenya da dama.