Joe Biden: Yadda za a rantsar da sabon shugaban Amurka da mataimakiyarsa

Biden and Harris

Asalin hoton, Getty Images

Zaɓaɓɓen Shugaban Amurka Joe Biden ba zai shiga Fadar White House ba har sai ranar da aka rantsar da shi - za a gudanar da fareti da sauran abubuwa yayin da za a rantsar da zaɓaɓɓen shugaban da kuma mataimakiyarsa Kamala Haris.

Tun daga batun dokokin korona da batun tsaro da kuma batun zuwan mawaƙiya Lady Gaga, ga duka abin da ya kamata ku sani game da wannan babbar rana.

Mene ne bikin rantsarwa?

Bikin rantsarwa biki ne da ake gudanar da shi a hukumance da yake alamta ranar farko da shugaban ƙasa zai fara aiki, kuma ana gudanar da bikin ne a birnin Washington DC.

Abin da ake buƙata daga shugaban ƙasar kawai shi ne ya karanta kalmomin rantsuwar kama aiki inda zai rantse da cewa zai gudanar da aikinsa bisa gaskiya da amana kamar yadda kundin tsarin mulkin ƙasar ya tanada.

Da zarar ya kammala rantsuwar, Mista Biden zai fara aiki a matsayin zaɓaɓɓen shugaban Amurka na 46, sai dai bayan nan akwai wasu shagulgula da za su biyo baya

Ita ma Kamala Harris za ta zama mataimakiyar shugaban ƙasa a ranar bayan ta sha rantsuwa, kuma an saba fara rantsar da mataimaki kafin shugaba a ƙasar.

Yaushe ne za a rantsar da Biden?

A doka, za a rantsar da shugaban ne a ranar 20 ga watan Janairu. Za a a fara jawabai na buɗe taro da misalin 11:30 agogon EST, kimanin 16:30 kenan agogon GMT inda ake sa ran da misalin 12:00 na ranar agogon EST za a rantsar da Biden da Kamala.

Ana sa ran da yammaci ko zuwa dare Mista Biden zai koma White House - inda a nan ne zai zauna har wasu shekaru huɗu masu zuwa

Ya yanayin tsaro zai kasance a ranar?

Kamar yadda aka saba, ana tsaurara tsaro a duk lokacin bikin rantsar da shugaban ƙasa, ana ganin a wannan karon za a ƙara tsaurara tsaro musamman bayan wasu magoya bayan Donald Trump sun kutsa Majalisar Tarayyar Amurka a ranar 6 ga watan Janairu.

.

Asalin hoton, Getty Images

Jami'an ƙasar sun ƙara tsaurara tsaro tare da rufe wasu sassa na birnin na Washington. Jami'an tattara bayanan sirri tuni suka ɗauki nauyin kula da shirye-shiryen tsaro, inda suke da goyon bayan wasu sojojin tarayyar ƙasar har mutum 15,000 da kuma ƙarin dubban ƴan sanda.

Tuni aka saka dokar ko-ta-kwana a Washingtin DC, kuma birnin zai ci gaba da zama a hakan har sai bayan rantsuwa.

Wani jami'i da ake kira Matt Miller, wanda shi ne ke jagorantar tabbatar da tsaro yayin rantsuwar a madadin hukumar tattara bayanan sirrin, ya shaida wa ƴan jarida cewa an shafe kusan shekara guda ana gudanar da shirye-shiryen.

Shin Trump zai halaraci bikin rantsuwar?

Ya zama kamar al'ada ga shugaban ƙasa mai barin gado ya halarci bikin rantsuwar, sai dai a bana, abin zai bambanta domin Shugaba Trump ya bayyana cewa ba zai je wurin ba.

"Ga duka masu tambaya, ba zan je wurin bikin rantsuwa ba a ranar 20 ga watan Janairu," kamar yadda Mista Trump ya wallafa a shafinsa na Twitter a ranar 8 ga watan Janairu. Ana sa ran cewa shugaban zai tafi gidansa na Florida a ranar.

Wasu daga cikin magoya bayan Trump ɗin sun ce za su haɗa bikin ranstuwa na biyu a ranar amma ta intanet a daidai lokacin da ake rantsar da Biden ɗin.

Sama da mutum 68,000 a shafin Facebook sun bayyana cewa za su halarci bikin rantsuwar ta intanet domin nuna goyon bayansu ga Trump.

Donald Trump and Barack Obama

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, A shekarun baya dai Barack Obama ya halarci bikin rantsar da Trump

A lokacin da aka rantsar da Mista Trump, Hillary Clinton ta raka mijinta Bill Clinton zuwa bikin rantsuwar - watanni biyu kacal bayan Mista Trump ya kayar da ita a zaɓen shugaban ƙasar.

Shugabannin Amurka uku kacal a tarihi suka ƙi yarda su halarci bikin rantsuwar wanda zai karɓe su - John Adams da John Quincy Adams da kuma Andrewa Johnson, sai dai a shekaru 100 da suka gabata ba a samu shugaban dai ya yi haka ba sai a yanzu aka samu Shugaba Trump.

Sai dai mataimakin shugaban ƙasa, Mike Pence ya bayyana cewa zai halarci taron.

Ta ya annobar korona za ta sauya bikin rantsuwa na bana?

A baya dai, akan ga ɗaruruwan mutane na shiga birnin Washington DC - an yi ƙiyasin cewa mutum miliyan biyu sun je birnin a lokacin rantsar da Obama a 2009.

Sai dai a wannan karon za a ƙayyade adadin mutanen da za a bari, kamar yadda waɗanda ke tare da Mista Biden suka bayyana, haka kuma sun roƙi Amurkawa da kada su yi tururuwa zuwa babban birnin ƙasar, haka kuma tun bayan da aka kutsa a Majalisar Tarayyar Amurka, hukumomi a ƙasar sun sha nanata irin wannan kira.

Jaridar Washington Post ta ruwaito cewa kusan mutum 200 ne za su zauna a wurin, kuma tare da ba juna tazara.

Kowa zai saka takunkumi kuma kowa za a yi masa gwajin korona kwanaki kafin wannan biki. Tun a watan Yunin bara Mista Biden ya ce ba zai saka takunkumi ba idan za a rantsar da shi.

.

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Tuni aka fara shirya wurin da za a gudanar da bikin rantsuwar

A baya dai, sama da tikiti dubu 200 ake sayarwa domin halartar wannan gagarumin biki, sai dai sakamakon ƙaruwar cutar korona a faɗin Amurka, tikiti dubu kaɗai za a sayar.

A wannan shekara, kamar yadda aka saba miƙa mulki cikin ruwan sanyi, sabon shugaban zai yi zagaye domin duba sojojin da suke fareti.

Sai kuma daga nan za a raka Mista Biden da kuma Ms Harris da iyalansu zuwa White House inda sojoji ne za su yi rakiyar da kaɗe-kaɗe.

Waɗanne mawaƙa za su yi wasa a wurin?

A shekarun da suka gabata, shugabannin da za a rantsar kan saka wasu sahararrun mawaƙa a cikin waɗanda za su yi wasa yayin bikin, sai dai a bana duk da annobar korona, lamarin bai kasance daban ba.

Mawaƙiya Lady Gaga - wadda shahararriyar mawaƙiya ce kuma mai goyon bayan shugaban ƙasar - za ta rera taken ƙasar inda Jennifer Lopez za ta rera waƙa yayin bikin.

Bayan an rantsar da Mista Biden, tauraron fina-finan nan Tom Hanks, zai yi wani shiri na musaman a talabijin duk domin nuna murna.

Cikin waɗanda za su shiga shirin na talabijin, akwai Jon Bon Jovi da Demi Lovato da kuma Justin Timberlake inda kuma kusan duka manyan kafofin talabijin na Amurka za su haska shirin, sai dai tashar Fox News ba za ta haska shirin ba, wadda tasha ce da aka santa wurin goyon bayan Mista Trump.