Kamala Harris: Wace ce abokiyar takarar Joe Biden a zaɓen Amurka na 2020?

Kamala Harris

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kamala Harris za ta samu dama ta biyu ta shiga fadar White House a bana bayan Joe Biden ya dauko ta don mara masa baya

Watanni bayan burinta na zama 'yar takarar shugaban ƙasa ya tunkuyi burji, a yanzu Kamala Harris ta samu wata damar yin takara ƙarƙashin inuwar jam'iyyar Dimokrat.

Bara ne, sanatar daga jihar California ta yi wani gagarumin yunƙuri zuwa gaban wani fagen 'yan takara kuma ta yi wani namijin ƙwazo yayin muhawara - da kuma kakkausar sukar da ta yi wa abokin fafatawarta Joe Biden kan batun launin fata.

Sai dai zuwa ƙarshen 2019, sai yaƙin neman zaɓenta ya kwanta dama.

A yanzu, tare da Mista Biden, wanda ake ɗauka shi ne dan takarar jam'iyyar Dimokrat, matar mai shekara 55 za su yi tafiya tare a matsayin mataimakiyar ɗan takarar shugaban ƙasa.

Bari mu yi nazari kan rayuwar Kamala Harris, yayin da take fuskantar ƙalubale iri daban-daban a kan hanyarta ta shiga fadar White House.

Wace ce Kamala Harris?

An haifi 'yar jam'iyyar Dimokrat din ce a Oakland, cikin jihar California, iyayenta 'yan ci-rani ne: mahaifiyarta 'yar asalin ƙasar Indiya, sai mahaifinta haifaffen Jamaika.

Bayan mutuwar auren mahaifanta, sai babarta wadda Hindu ce kuma ƙwararriya kan sha'anin cutar kansa, mai fafutukar tabbatar da 'yancin jama'a ta riƙe Kamala Harris.

Ta taso ne cikin riƙo da tushenta na Indiyawa, inda ta riƙa bin mahaifiyarta suna zuwa ziyara ƙasar, sai dai Kamala ta ce babarta ta rungumi al'adun Amurkawa 'yan asalin Afirka a Oakland, kuma ta tsoma 'ya'yanta mata biyu - Kamala da ƙanwarta Maya - ciki.

"Mahafiyata ta fahimta sosai cewa tana goyon 'ya'ya mata baƙaƙen fata biyu ne," kamar yadda ta rubuta a littafin tarihinta mai suna (The Truths We Hold).

"Ta san cewa ƙasar da ta karɓa za ta kalli Maya da ni a matsayin 'yan mata baƙaƙen fata ne don haka ta ƙuduri niyyar tabbatar da ganin mun tashi cikin ƙarfin gwiwa da alfaharin zama mata baƙaƙen fata."

Kamala Harris campaign signs

Asalin hoton, Getty Images

Ta dai ci gaba da karatu har zuwa Jami'ar Howard, ɗaya daga cikin jami'o'i da kwaleji-kwalejin Amurka na baƙar fata da suka tsere sa'a a tarihi, kuma ta bayyana gogewar da ta samu a matsayin daya daga cikin mafi tasiri a shekarunta na ƙuruciya.

Kamala Harris ta ce a ko da yaushe tana cike da gamsuwa da asalinta kuma kawai tana bayyana kanta ne a matsayin "Ba'amurkiya".

A 2019 ta fada wa jaridar Washington Post cewa bai kamata 'yan siyasa su ware kansu saboda launin fatarsu ko kuma asalin tushensu ba.

Wannan layi ne

Muƙaman data riƙe a bangaren doka da oda

Bayan ta shafe shekara huɗu a Jami'ar Howard, Kamala Harris ta wuce don samun digirinta kan fannin shari'ah a Jami'ar California, Hastings.

Kuma a nan ne ta fara aikinta a Ofishin Lauyan Gwamnati mai kula da Lardin Alameda.

Ta zama lauyar gwamnatin lardi - wato babbar mai shigar da ƙara - a birnin San Francisco cikin 2003.

Kafin a zabe ta matsayin mace ta farko kuma Ba'amurkiya 'yar asalin Afirka ta farko da ta riƙe muƙamin babbar lauya a California kuma babbar jami'ar tabbatar da doka a jihar Amura mafi yawan jama'a.

A kusan wa'adi biyu da ta yi a ofishin babbar lauyar gwamnati, Kamala ta yi fice a matsayin daya daga cikin taurari masu tasowa na jam'iyyar Dimokrat.

Kuma ta yi amfani da wannan ɗaukaka ta cicciɓa zabenta zuwa ƙaramar 'yar majalisar dattijan Amurka daga jihar Kalifoniya a 2017.

US Senator Kamala Harris

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Lokacin da take Majalisar Dattijan Amurka Kamala Harris ta samu yabo saboda salon tambayoyinta na masu shigar da ƙara a kotu

Tun bayan zaɓenta zuwa majalisar dattijan Amurka, tsohuwar mai shigar da ƙarar ta zama 'yar gaban goshi a tsakanin masu ra'ayin kawo sauyi .

Kaifin tambayoyinta ga mutumin da aka ba da sunansa don zama alƙalin Kotun Ƙoli Brett Kavanaugh da kuma Babban Lauyan Gwamnati William Barr a lokacin muhimman zaman sauraron bahasi na Majalisar Dattijai sun ja mata ƙwarjini.

Wannan layi ne

Burin shiga Fadar White House

Lokacin da ta ƙaddamar da neman takararta na shugabancin ƙasa ga taron mutane sama da 20,000 a Oakland, cikin jihar California, a farkon shekarar da ta wiuce, yunƙurinta na shekara ta 2020 ya gamu da matuƙar ɗokin jama'a tashin farko.

Sai dai sanatar ta gaza fayyace azancin da take da shi ƙarara na shiga takara, kuma ta riƙa hargitsa amsoshinta ga tambayoyin da aka yi mata kan muhimman manufofi a ɓangarori irinsu kula da lafiya.

Ta kuma gaza amfani da ƙwaƙƙwaran makin da ta samu kan ƙwazon da ta yi wajen muhawarar 'yan takara, inda ta nuna ƙwarewarta ta masu shigar da ƙara kotu, sau da yawa Joe Biden sai koma yana suka.

'Yar jam'iyyar Dimokrat daga Kalifoniya da ke da ƙwarewar aikin jami'ar tabbatar da doka, Kamala Harris ta yi ƙoƙarin iya ruwanta tsakanin ɓangaren masu ra'ayin sauyi da masu sassaucin ra'ayi na jam;iyyar.

Sai dai ta gaza jan hankalin kowanne ɓangare, inda ta kawo ƙarshen takararta a watan Disamba kafin zaɓen fitar da gwanin jam'iyyar Dimokrat na farko a Iowa.

A watan Maris ne kuma, Kamala Harris ta bayyana goyon bayanta ga tsohon mataimakin shugaban ƙasar, inda ta ce za ta yi "duk abin da za ta iya cikin ikonta don taimaka masa cin zaɓen shugaba ƙasa mai zuwa a Amurka".

Wannan layi ne

Tarihinta kan aikin 'yan sanda da yaƙi da laifuka

Takarar Kamala Harris a 2020 ta janyo haska fitila kan abubuwan da ta cimma lokacin da take riƙon muƙamin babbar mai shigar da ƙara ta Kalifoniya.

Duk da goyon bayanta kan manufofin kawo sauyi ga batutuwa irinsu auren jinsi da hukuncin kisa, ta fuskanci jerin suka daga masu ra'ayin kawo sauyi.

Saboda rashin zama cikakkiyar 'yar kawo sauyi kuma ta zama abar suka cikin sharhin kunyatawa na wata malamar shari'a ta Jami'ar San Francisco, Lara Bazelon.

Ta rubuta a farkon yaƙin neman zaɓen Kamala cewa akasari sanatar ta riƙa noƙewa baya a gwagwarmayar masu ra'ayin kawo sauyi da ta ƙunshi batutuwa kamar yi wa aikin 'yan sanda garambawul.

Da sauye-sauye kan yaƙi da ta'ammali da ƙwaya da kuma kuskuren yanke hukunci.

Kamala Harris and Joe Biden at a Biden campaign event

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, After quitting the race in January, Ms Harris endorsed Joe Biden two months later

"Mai shigar da ƙara 'yar ra'ayin kawo sauyi" kamar yadda take bayyana kanta ta yi ƙoƙarin jaddada nasarorin da ta cimma.

Nasarorin da suka fi rinjaya zuwa ra'ayin sauye-sauye da ke buƙatar sanya kyamarori a jikin wasu jami'an tsaro na musamman a Ma'aikatar Shari'ah ta Kalifoniya.

Ita ce jihar farko da ta amincewa yin amfani da wannan tsari da kuma ƙaddamar da wani rumbun adana bayanai da ke bai wa mutane damar samun ƙididdigar laifukan da aka aikata - amma duk da haka ta gaza samun karɓuwa.

"Kamala 'yar sanda ce" da akasari aka guje ta lokacin yaƙin neman zaɓe, inda ta ɓarar da damarta ta shawo kan ƙarin masu ra'ayin sassauci na jam'iyyar Dimokrat yayin zaɓen fitar da gwani.

Sai dai waɗannan nasarori da ta cimma a matsayinta na jami'ar tsaro, na iya zama masu amfani a babban zaɓe na ƙasa lokacin da Dimokrat ke buƙatar shawo kan ƙarin masu matsakaicin ra'ayi da mutanen da ba ruwansu da jam'iyya don kada mata ƙuri'u.

Yanzu kuma, Amurka na fama da sakamakon matsalar wariyar launin fata, ana kuma bin diddigi kan matsalar cin zalin 'yan sanda.

Kamala Harris ta shiga gaba, inda za ta yi amfani da lasifikarta wajen kambama muradan masu ra'ayin kawo sauyi.

Wannan layi ne