Zaben Amurka na 2020: Ko ka samu rinjayen ƙuri'un jama'a ba lallai ka kai labari ba

US voter at booth

Asalin hoton, Getty Images

Za a gudanar da zaɓen shugaaban Amurka cikin ƙasa da kwana 100. Sai dai mai yiwuwa ne ɗan takarar da ya samu rinjayen ƙuri'u daga jama'a, ba shi ne zai lashe zaɓen ba.

Wannan na faruwa ne saboda ba kai tsaye masu kaɗa ƙuri'a ke zaɓar shugaban ƙasa ba, sai dai ta hanyar abin da ake kira rukunin masu zaɓe.

Section divider

To wa Amurkawa ke zaɓa?

Idan Amurkawa suka je rumfunan kaɗa ƙuri'a yayin zaɓukan shugaban ƙasa, haƙiƙa suna zaɓar ayarin wasu jami'ai ne waɗanda su ne ke haɗuwa su samar da rukunin masu zaɓar shugaban ƙasa wato electoral college.

Abin da kalmar "college" a nan take nufi shi ne wani ayarin mutanen da aka ɗora alhakin wani aiki. Waɗannan mutane su ne masu zaɓe, aikinsu shi ne su zaɓi shugaban ƙasa da kuma mataimakinsa.

Rukunin masu zaɓen na gamuwa ne duk bayan shekara huɗu, makwanni ƙalilan bayan ranar babban zaɓe, don gudanar da wannan aiki.

Section divider

Yaya tsarin rukunin masu zaɓe yake aiki?

Adadin masu zaɓe daga kowacce jiha ya dogara ne a kan yawan jama'arta.

Akwai jimillar masu zaɓe 538 a Amurka.

Jihar California ce ke da masu zaɓe mafi yawa da mutum 55, yayin da jihohi masu yawan jama'a kaɗan irinsu Wyoming da Alaska da North Dakota (da kuma Washington DC) ke da mafi ƙarancin masu zaɓe mutum uku.

Kowanne mai zaɓe yana wakiltar ƙuri'a guda ɗaya ne, kuma ɗan takara yana buƙatar samun rinjayen ƙuri'un, wato ƙuri'a 270 ko fiye don samun nasarar zama shugaban ƙasa.

line
Electoral college map
line

Ɗaukaci dai, jihohi na sadaukar da dukkan ƙuri'un rukunin masu zaɓensu ne ga duk wanda ya yi nasara a zaɓen da al'ummar jihar ta kaɗa ƙuri'a.

Ga misali, idan ɗan takarar jam'iyyar Rifablikan ne ya lashe kashi 50.1% na ƙuri'un Texas, shi ke nan ya lashe illahirin ƙuri'un rukunin masu zaɓen jihar 38.

Akwai jihohi guda biyu kawai (Maine and Nebraska) da ke raba ƙuri'un rukunin masu zaɓensu gwargwadon yawan ƙuri'un da kowanne ɗan takara ya samu.

Wannan ta sa 'yan takara suka fi mayar hankali kan taƙamaimai "jihohin da ke da gagarumin tasiri" - inda ƙuri'u na iya karkata kowanne ɓangare - maimakon su yi ƙoƙarin cin ƙuri'u masu yawan gaske a faɗin ƙasar.

Duk jihar da suka ci tana daɗa kusantar da su kai wa ga samun ƙuri'a 270 da suke buƙta daga rukunin masu zaɓe.

Section divider

Kana iya samun rinjayen ƙuri'un jama'a amma ba ka yi shugaban ƙasa ba?

Eh, hakan na iya faruwa.

Abu ne mai yiwuwa 'yan takarar da suka ci mafi yawan ƙuri'un jama'a a faɗin ƙasar, amma su gaza samun isassun jihohin da za su ba su damar cin ƙuri'a 270 ta rukunin masu zaɓe.

Haƙiƙanin gaskiya ma, biyu cikin zaɓe biyar na baya-bayan nan 'yan takarar da suka yi galaba su ne suka samu ƙuri'u mafi ƙaranci a zaɓen jama'ar gari a kan abokan fafatwarsu.

A shekara ta 2016, Donald Trump ya gaza abokiyar fafatawarsa Hillary Clinton da kusan ƙuri'a miliyan uku, amma ya ci shugaban ƙasa saboda rukunin masu zaɓe sun kaɗa masa rinjayen ƙuri'u.

George Bush in 2000

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Ɗan takarar jam'iyyar Rifablikan George W Bush ne ya lashe zaɓen shekara ta 2000 kan abokin fafatawarsa na Dimokrat, Al Gore

A 2000, George W Bush ya lashe ƙuri'a 271 ta rukunin masu zaɓe, duk da yake ɗan takarar jam'iyyar Dimokrat Al Gore ne ya yi nasara a zaɓen jama'ar gari ta yawan ƙuri'u fiye da rabin miliyan.

Akwai sauran shugabannin Amurka uku da aka zaɓa ba tare da sun ci zaɓen jama'ar gari ba, dukkansu a Ƙarni na 19: John Quincy Adams da Rutherford B Hayes da kuma Benjamin Harrison.

Section divider

Me ya sa aka zaɓi wannan tsari?

Lokacin da ake fitar da daftarin tsarin mulkin Amurka a shekarar 1787, wani zaɓen jama'ar gari don fitar da mutumin da zai shugabanci ƙasar a zahiri ya gaza yiwuwa. Hakan ta faru ne saboda girman ƙasar da kuma wahalar harkokin sadarwa.

A lokacin kuma, ana ɗari-ɗarin bai wa 'yan majalisar dokokin da ke Washington DC damar zaɓar shugaban ƙasa.

Don haka, masu tsara daftarin tsarin mulki suka ƙirƙiri tsarin rukunin masu zaɓe, inda kowacce jiha take fitar da masu zaɓenta.

Ƙananan jihohi sun fi maraba da tsarin don kuwa ya ba su ƙarin amo fiye da ƙuri'un jama'ar faɗin ƙasar wajen tabbatar da wane ne shugaban ƙasa.

Haka zalika, jihohin kudancin Amurka sun fi haba-haba da tsarin rukunin masu zaɓe, inda bayi suke da gagarumin yawa a tsakanin jama'a. Duk da yake, bayin ba sa zaɓe amma ana ƙirga su cikin harkokin ƙidaya na Amurka.

Tun da ana tantance yawan ƙuri'un rukunin masu zaɓe da girman al'ummar jiha ne to jihohin kudanci sun fi tasiri wajen zaɓar shugaban ƙasa kan abin da za su samu daga zaɓen jama'ar ƙasa kai tsaye.

Electoral map

Asalin hoton, Getty Images

Bayanan hoto, Kowacce jiha tana da adadin ƙuri'un da ke wakiltarta a tsarin rukunin masu zaɓe
Section divider
Presentational grey line