Zaben Amurka na 2020: Biden ya zabi bakar fata Kamala Harris a matsayin mataimakiyarsa

Kamala Harris standing in front of an American flag

Asalin hoton, Getty Images

Dan takarar jam'iyyar Democrat a zaben Amurka Joe Biden ya zabi Sanata Kamala Harris a matsayin mataimakiyarsa a zaben kasar da za a yi a watan Nuwamba. Ita ce mace bakar fata ta farko da aka tsayar takara a wannan matsayi a tarihin Amurka.

'Yar majalisar dattawan da ke wakiltar jihar California ta taba neman a tsayar da ita takarar shugabancin kasar, kuma 'yar asalin India da Jamaica ce.

Ita tsohuwar babbar mai shari'a a jihar California inda ta dade tana kira a yi garambawul ga dokokin 'yan sanda a yayin da ake zarginsu da nuna wariyar launin fata.

Mr Biden zai fafata da Shugaba Donald Trump a zaben da za a gudanar ranar 3 ga watan Nuwamba.

Mataimakin shugaban kasa Mike Pence shi ne dan takarar mukamin na jam'iyyar Republican.

Mr Biden ya wallafa sakon Twitter da ke cewa "abin alfahari ne a gare ni" da na zabi Ms Harris a matsayin mataimakiyata.

Ya bayyana ta a matsayin "mai fafutuka maras tsoro, kuma daya daga cikin ma'aikatan gwamnati mafi inganci a kasar nan".

Mr Biden ya bayyana yadda ta yi aiki kut da kut da marigayi dansa, Beau, lokacin tana kan mukamin antoni janar.

"Na kalli yadda suka fafata da manyan bankuna, suka tallafawa ma'aikata, sannan suka kare martabar mata da kananan yara," in ji sakon nasa na Twitter.

"Na yi alfahari a wancan lokacin, kuma yanzu ina alfahari da kasancvewarta abokiyar takarata."

Ana kallon Ms Harris, mai shekara 55, a matsayin wacce tauraruwarta take haskakawa a jam'iyyar Democrat, ko da yake ta fasa shirinta na takarar shugabancin kasar a watan Disamba.

Ta sha yin musayar yawu da Mr Biden lokacin muhawarar zaben fitar da gwani na wanda zai tsayawa jam'iyyar takara.

Bayanan bidiyo, Harris da Biden sun sha yin musayar baki

Wace ce Kamala Harris?

An haifi 'yar jam'iyyar ta The Democrat a birnin Oakland, na California kuma dukkan iyayenta bakin haure ne: mahaifiyarta 'yar asalin India yayin da mahaifinta dan asalin kasar Jamaica ne.

Ta yi karatun jami'a a Jami'ar Howard, daya daga cikin jami'o'in da bakaken fata suka fi halarta. Ta bayyana zaman da ta yi a jami'ar a matsayin daya daga cikin manyan darussa da ta koya a rayuwarta.

Ms Harris ta ce a ko da yaushe tana alfahari da kasancewarta bakar fata kuma tana bayyana kanta a matsayin "Ba'amurkiya".

A shekarar 2019, ta shaida wa jaridar Washington Post cewa bai kamata a auna 'yan siyasa da launin fatarsu ko asalinsu ba. "Abin da nake na na fada shi ne: Na san kaina. Kuma na gamsu da hakan," in ji ta.

Karin labarai da za ku so ku karanta: