Martin Luther King: Kalli hotunan tarihi na fafutukar ƙwato wa baƙaƙen fata ƴanci a Amurka
Yau Juma'a ne ake cika shekara 92 da haihuwa Martin Luther King - kuma bayan dogon bincike, Jordan J Lloyd ya sanya kala a hotunan da asalinsu aka dauka a fari da baƙi na Dr King da sauran sanannun mutane da suka yi fafutukar ƙwato ƴancin bakaken fata a Amurka a shekarun 1960.

Asalin hoton, Library of Congress / Jordan J. Lloyd
"Mutane na da damar sanin tarihinsu," Lloyd ya shaida wa BBC.
"Kuma kala na cire duk wasu shakku da ke tsakaninmu da tarihinmu,
"Lokaci guda, sai ka ga hotunan kamar gaske."

Asalin hoton, Library of Congress


Asalin hoton, Library of Congress / Jordan J. Lloyd

Asalin hoton, Library of Congress / Jordan J. Lloyd
A 1963, wani gangamin mutane 250,000 ne suka yi tattaki na lumana a Washington don jawo hankali kan rashin adalci da ake nuna wa bakar fata da kuma fatan matsa wa majalisa lamba ta amince da dokar hana nuna wariyar launin fata wadda Shugaba John F Kennedy ya shigar.

Asalin hoton, Library of Congress / Jordan J. Lloyd
Gangamin ya ja hankalin kafofin watsa labarai a faɗin duniya - amma gwamnatin tarayya ba ta ɗauki wani matakin gyara ƙorafe-ƙorafen da aka yi ba.
"Ana samun ci gaba ne ta hanyar yin fafutuka," in ji Lloyd.
"Kuma ina ganin mutane da yawa a yau na iya ganin kamanceceniya tsakanin rashin daidaiton da ya faru a shekarun 1960 da yanzu."

Asalin hoton, Library of Congress / Jordan J. Lloyd
Lloyd ya samo hotunan ne daga Library of Congress, wato ɗakin ajiyar littafai na majalisar Amurka - amma bincikensa ya gano wasu hotuna masu kala da aka ɗauka a lokacin gangamin.
"Ɗaukar hoto mai kala a wancan lokacin na da matuƙar tsada," a cewarsa.
"Kuma yanzu, ana iya amfani da hotunan ne kawai ta hanyar sayen wani lasisi mai tsadar gaske.

Asalin hoton, Library of Congress / Jordan J. Lloyd
"Batun launin fata batu ne mai sarƙaƙiya.
"Haka kuma shi ne abin da muke fara gani idan muka ga hotuna a karon farko.
"Launin fatar mutane ya danganta da ƙabila da shekaru, wanda ya kamata a lura da shi tare da yadda aka haska hoton da yanayin ranar da aka yi hoton.
"A waɗannan hotunan, muna iya gane yanayin da ake ciki a ranar ta hanyar lura da abubuwa kamar inuwa da rahotonnin yanayin ranar tattakin.

Asalin hoton, Library of Congress / Jordan J. Lloyd


Asalin hoton, Library of Congress / Jordan J. Lloyd
"Masu sukar hotuna masu kala na haɗa sakamakon wasu ayyuka na fasaha kamar ƙirkirarriyar basira wato Artificial Intelligence, sai su ce ai an lalata tarihi.
"Ni a ganina, wahalar da aka sha wajen gyara hotunan da bincike a kansu da sanya masu kala ya cancanci a ce ya tagaza wa tarihi, maimakon a ce ya sauya shi.
"Ana iya yi wa abin da ake da masaniya a kai kallo da wata mahanga ta daban."
"Gangamin yaƙin daina wariyar launin fata na civil rights movement na da matuƙar muhimmanci a tarihin Amurka amma sai aka ware masa wasu 'yan hotuna marasa kala a littafan makaranta da shafukan intanet."

Asalin hoton, Library of Congress / Jordan J. Lloyd
Hotunan Lloyds na nan a shafin Unsplash kuma ana iya amfani da su kyauta.
"Wannan ɓangare mai muhimmanci a tarihin Amurka ya cancanci mutane su gan shi kuma a yaɗa shi sau da yawa, ko a aji ko a fasta ko bangon littafai da dai sauransu," a cewarsa.

Asalin hoton, Library of Congress / Jordan J. Lloyd










