Donald Trump: Yadda shafukan sada zumunta suka 'rufe bakin' shugaban Amurka

    • Marubuci, Daga Joe Tidy
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Cyber reporter

Idan kun taba tantama a kan karfin ikon manyan kamfanonin sada zumunta, to lallai durkushewar shafin Parler ranar Litinin na iya nuna maku wani abu.

Kamar sauran mutane, na leka shafin na sada zumunta don ganin abin da zai faru bayan karfe 11:59 agogon Pacific na Amurka.

Wannan ne iya wa'adin da kamfanin Amazon ya bai wa manhajar ta Parler, ya ce ya nemi mai mara masa baya kafin ya yi waje rod da shi saboda yada bayanai masu tunzura tashin hankali.

Ana ganin wannan a matsayin wani lokaci mai muhimmanci a yunkurin da manyan kamfanonin fasaha na Amurka ke yi wajen ganin sun hana Donald Trump da magoya bayansa masu tsattsauran ra'ayi damar amfani da shafukan sada zumunta bayan zanga zangar da aka yi a zauren majalisar dokokin kasar na Capitol Hill cikin makon da ya wuce.

Karfe sha biyu ta yi kuma babu abin da ya faru. Da ni da sauran miliyoyin masu amfani da shafin na Parler mun ci gaba da amfani da shi kamar yadda muka saba. Amma kan ka ce kwabo, sai masu amfani da shafin suka fara samun matsala wajen tura bayanai. Ni dai kusan karfe 12:10, sai komai ya daina aiki.

Kamar kiftawar ido, shafin Parler, wanda ke da dimbin masu amfani da shi, kuma wanda ake ganin ya fi Twitter ba da damar bayyana ra'ayi, ya daina aiki. Na wannan lokacin dai.

Parler na iya samun sabon kamfanin da zai mara masa baya amma rasa Amazon Web Services (AWS) kamfanin da ke samar da hanyoyin intanet mafi girma a duniya, na nufin wasu kamfanonin irinsa na iya juya wa Parler baya.

Ba sabon abu ba ne

Wata mai bincike kan fasaha Stephanie Hare ta ce ba wannan ne karon farko da wani babban kamfanin fasaha na Amurka ya cire shafin sada zumunta bisa irin wannan dalilin ba.

"Matakin da Amazon ya dauka a kan Parler ba sabon abu ba ne, kamar yadda muka ga kamfanonin Amurka irin su Cloudfare sun cire hanyoyin aika sakkoni a shafin The Daily Stormer na masu tsananin kishin farar fata a shekarar 2017 da 8Chan a shekarar 2019 bayan da wani dan bindiga ya yi amfani da shafin ya aika sakonni kafin ya kai hari a garin El Paso da ke Texas," a cewarta.

Ba AWS ne kawai ya dauki mataki a kan Parler ba. Google da Apple ma sun goge shafin daga shafukansu na sayen manhaja. Wannan ma ba sabon abu ba ne.

Gab, wani shafi da ke ikirarin mai bai wa mutane damar bayyana ra'ayinsu amma an zarge shi da zama wajen baje kolin masu tsattsauran ra'ayi, shi ma an goge shi daga app store na sayen manhajoji. Sai dai ana iya shiga shafin ba ta manhaja ba sai dai ta hanyar binciko shi a intanet. An kuma ce yana kara samun masu amfani da shi a 'yan kwanakin nan.

A wani bangare na cire shafukan da ke da alaka da harin da aka kai zauren majalisar Amurka, ranar Litinin Twitter ya sanar da cewa ya sauke shafukan mutane sama da 70,000 da ke da alaka da mabiya Donald Trump na QAnon.

Haka kuma, Facebook ya ce zai cire duka wasu sakonni da ke dauke da kalaman "Stop the Steal" - taken da Mista Trump ke amfani da shi kan zarginsa na magudin zaben kasar da aka yi a watan Nuwamba da ta wuce.

Haramci mai matsala

Sai dai abin da ba a saba gani ba shi ne yadda aka yi wa Shugaban kasar.

Tun da magoya bayan Mista Trump suka kai hari Capitol a makon jiya, an haramta masa amfani da wasu daga cikin manyan shafukan sada zumunta ciki har da Twitter da Facebook da Instagram da Snapchat da Twitch.

Youtube ya goge wasu bidiyoyinsa amma an masa gargadin cewa an bashi dama ta karshe.

Shugabannin Turai ciki har da Shugabar Jamus. Angela Merkel, ta bayyana matakin a matsayin mai matsala.

Kwamishinan hukumar Tarayyar Turai, Thierry Breton, ya bayyana rikicin da ya faru a Capitol Hill a matsayin "harin 9/11 a shafukan sada zumunta". Ya ce "Idan har shugaban Twitter zai iya korar Shugaban Amurka daga shafinsa lallai akwai babbar matsala".

Sakataren harkokin lafiya na Birtaniya, Matt Hancock, ya ce yanzu shafukan sada zumunta na daukar matakan da bai dace su dauka ba.

Yayin da Alexei Navalny, dan siyasa a Rasha kuma sanannen mai sukar Shugaba Vladimir Putin ya alakanta haramcin Mista Trump a Twitter da tauye hakkin fadar ra'ayi.

Ya wallafa sako kamar haka a shafinsa na Twitter: "Haramta wa Donald Trump amfani da Twitter bai dace ba. Lallai ne Twitter kamfani ne mai zaman kansa, amma mun ga misalai da dama a Rasha da China inda irin wadannan kamfanonin suka zama aminan gwamnati idan aka zo batun tauye hakkin fadar ra'ayi."

Cutar korona ta sauya shafukan sada zumunta

Gaskiyar Magana it ace shafukan sada zumunta kamfanoni ne masu zaman kansu. Kamar yadda kungiya mai zaman kanta za ta gindaya sharuddanta ga mambobinta, haka ma Mark Zuckerberg na Facebook ko Jack Dorsey na Twitter.

Doka guda mai muhimmanci da aka sa ita ce a rika bai wa sakonnin da 'yan siyasa ke wallafawa muhimmanci musamman kan yadda jama'a za su rika tattaunawa a kai.

Don haka shafukan ciki har Facebook da Twitter sun ce za su rika daga wa sanannun mutane kamar Shugaban Amurka kafa idan aka yi batun karya dokar masu amfani da shafuka.

Amma tun da annobar korona ta kunno kai abubuwa sun sauya matuka kuma kamfanonin sun sa ido sosai kan shugabannin duniya.

A watan Maris din bara, Facebook da Twitter sun goge wasu sakonnin Shugaban Brazil Jair Bolsanaro da na Shugaban Venezuela Shugaba Nicolas Maduro da suka kunshi bayanan bogi dangane da cutar korona.

Sai a watan Mayu ne Twitter ta dauki mataki shigen wannan kan Shugaban Amurka lokacin da ya sa wani gargadi a gaban wani sako da shugaban ya wallafa, inda Twitter ya ce sakon na goyon bayan tashin hankali.

Shugaban ya aika sako dangane da zanga zangar Black Lives Matter yana cewa:

"Idan aka fara sata a shaguna, za mu sa a fara harbin masu zanga zangar".

Mai sharhi kan shafukan sada zumunta Matta Navarra ya ce matakin haramta wa Mista Trump amfani da shafukan sada zumunta ya shata layi kan wanda zai rika amfani da shafukan da sakonnin da za a rika wallafawa.

Trump ya lashi takobin ramawa

Wasu masu sharhi na ganin cewa matakin na iya zama silar haifar da sa ido a shafukan zumunta a fadin duniya.

Ranar Litinin ne Facebook ya sanar da cewa ya goge wasu shafuka da ke da alaka da gwamnatin Uganda wanda kuma ake zargin ana amfani da su don shirya magudi a zaben kasar mai zuwa.

Lauya Whitney Merrill na ganin wannan matakin zai kawo sauyi a shafukan sada zumunta.

"Dokokin shafukan sada zumunta na sauyawa a hankali. Amma ba a amfani da su yadda ya kamata a fadin duniya. Ina tunain cire shugaban na iya zama silar ciccire masu irin wannan halayyar a fadin duniya."

A sa'o'insa na karshe a Twitter, Mista Trump ya sake zargin wani bangare na dokokin Amurka, bangare na 230 da "haramta" damar bayyana ra'ayi. A lokacin mulkinsa, ya yi barazanar soke dokar da ke kare shafukan sada zumunta daga daukar alhakin abin da masu amfani da su suka wallafa.

Mutane da dama na ganin cire wannan kariyar na iya kawo nakasu ga damar bayyana ra'ayi saboda dole shafukan su fara sa ido fiye da yadda suke yi yanzu.

Shugaba Joe Biden mai jiran gado, ya bayyana cewa shi ma zai so ya soke dokar don a kara sa ido sannan a hana labaran karya yaduwa.

A sakon na karshe da Mista Trump ya wallafa, ya ce yana tattaunawa da sauran shafuka kuma zai yi "wata muhimmiyar sanarwa nan ba da jimawa ba."

Idan abubuwan da suka faru a kwanankin nan za su iya zama wani abu, Mista Trump da magoya bayansa na fuskantar gwagwarmaya da 'yan majalisa da manyan kamfanonin fasaha kafin su iya samun wurin zama a shafukan na sada zumunta