Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Brexit: Burtaniya ta kammala ficewa daga Tarayyar Turai
Fafutukar da 'yan Burtaniya suka fara shekaru huɗu da rabi da suka gabata ta zamo gaske a daren Laraba, bayan da aka rattaba hannu a yarjejeniyar yanke alakar kasuwanci tsakanin Burtaniyar da EU.
Firai ministan Burtaniya, Boris Johnson ne ya sa hannu a kan yarjejeniyar kasuwanci tsakanin bangarorin biyu bayan ficewar Burtaniyar daga Tarayyar watanni 11 da suka gabata.
Majalisar wakilan kasar ce dai ta ta fara amincewa da yarjejeniyar ba tare da hamayya ba.
Sojojin yakin Burtaniya ne suka dauko kundin yarjejeniyar daga Brussels zuwa Burtaniyar inda firai minista Boris Johnson ya sanyawa hannu.
A makon da ya gabata ne dai Burtaniya da Tayyara Turai suka rattaba hannu kan yarjejeniyar da za ta fayyace alakar bangarorin biyu bayan ficewar Burtaniya daga EU.
Bisa wannan yarjejeniya, yanzu Burtaniya ta kammala ficewa daga kasuwar bai daya da shigi da fici na Tarayyar ta Turai.
Firai ministan kasar, Boris Johnson ya shaida wa BBC cewa yarjejeniyar na da matukar alfanu ga 'yan Burtaniya.
"Ina son kowa ya fahimci cewa wannan yarjejeniya da na sanya wa hannun yanzu ba it ace karshen al'amari ba.
Danba ne na kulla sabuwar alaka tsakanin Burtaniya da 'yan uwanmu da abokanmu da ke Turai. Jama'a al'amarin ya tabbata. Ga shi fa.
Na san tambayar da za ku yi it ace shin ko na karanta kundin. Amsar ita ce e na karanta. Kundi ne mai alherin gaske ga kasar nan har ma ga abokanmu da abokan huldarmu."
To sai dai abokan hamayya sun ce al'amarin ya yi kama da an gudu ba a tsira ba.
A watan Janairun shekarar nan ne Burtaniya ta fice daga tarayyar amma batun alakarta ta kasuwanci da EU ya hana ta sakat.
Tun dai tsakiyar shekarar 2015 Burtaniya ta fara fafutukar ficewa daga tarayyar ta turai amma sai a daren jiya Laraba ne mafarkinta ya tabbata na yanke alakar shekara 47.