Nasiru Kachalla: Abu biyar kan ƙasurgumin mai satar mutanen da aka kashe a Kaduna

Nasiru Kachalla

Asalin hoton, Kaduna State Govt

Bayanan hoto, Nasiru Kachalla ya daɗe yana kai hare-hare da satar mutane a wasu yankunan jihar Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna da ke arewa maso yammacin Najeriya ta tabbatar da mutuwar wani ƙasurgumin ɗan fashi kuma mai satar mutane da ya addabi jihar.

A wata sanarwa da kwamishinan tsaro da al'amuran cikin gida na jihar Samuel Aruwan ya fitar a ranar Litinin, ya ce an kashe Nasiru Kachalla ne a wani artabu tsakanin ɓangarorin ƴan bindigar biyu da suka addabi yankunan Kajuru da Chikun.

Mista Aruwan ya ce ƙungiyoyin wasu mutane da ke bayar da bayanan sirri sun tabbatar wa da gwamnatin cewa faɗan ya jawo an kashe miyagun da dama na dukkan ɓangarorin biyu, da suka haɗa da manyan yaran Kachalla.

An yi wannan artabu ne a wani daji da ke iyakar ƙananan hukumomin Kajuru da Chikun, kuma "mummunan rikicin" ya samo asali ne kan wasu garken shanu da suke taƙaddama a kai.

Ga dai wasu abubuwa biyar da kuke buƙatar sani kan Nasiru Kachalla

1. Kachalla ya daɗe yana wasan ɓuya tsakaninsa da jami'an tsaro kan wasu manyan laifuka da ya daɗe yana yi da suka haɗa da satar mutane don kuɗin fansa da kashe mutane da satar shanu da fashi da makami.

2. Kachalla da gungun mutanensa suna da hannu a cikin satar mutane da fashi da makami da aka sha yi, musamman na kan babban titin Kaduna zuwa Abuja da kuma na yankunan Chikun da Kajuru.

3. Shi ne ya kitsa sace wasu malaman Kirista na Cocin Good Shepherd Major Seminary a Kaduna a ranar 9 ga watan Janairun 2020, da kuma sace Mrs Bola Ataga da ƴaƴanta biyu da aka yi ranar 24 ga Janairun 2020.

Daga baya ƴan fashin na tawagar Kachalla suka kashe ɗaya daga cikin malaman cocin Michael Nnadi da kuma Mrs. Ataga, kafin su saki ƴaƴan nata.

4. Gungun mutanen Kachalla ne suka sace ɗalibai shida da malamai biyu na makarantar Engravers College a ƙauyen Kakau da ke ƙaramar hukumar Chikun ranar 3 ga watan Oktoban 2019.

5. A watan Afrilun 2020 jami'an tsaro sun kama mutum uku daga cikin gungun Kachalla da suka haɗa da Tukur Usman da Shehu Bello da kuma Mustapha Mohammed, a yayin da ake ci gaba da neman shugaban nasu.

Tawagar Kachalla

Asalin hoton, Kaduna State Govt

Bayanan hoto, Wasu mutum uku na tawagar Kachalla da jami'an tsaro suka kama a watan Afrilun 2020

Wasu labarai masu alaƙa

Wannan layi ne

Hari kan mafarauta da tare hanyar Giwa

A wani al'amarin daban kuma, gwamnatin Kadunan ta ce dakaru sun daƙile wani hari da ƴan fashi suka yi ƙoƙarin kai wa a kan hanyar Galadimawa zuwa Zariya, a ƙarƙashin ƙaramar hukumar Giwa.

Ƴan fashin sun tare hanyar na ƴan mintuna suna harbin kan mai uwa da wabi a lokacin da motoci ke wucewa.

"Tawagar Bataliya ta 4 ta sojojin Najeriya nan da nan suka bayyana a wajen. Suka tarwatsa ƴan fashin sannan kuma ba a sace ko jikkata kowa ba.

"Sojoji da ƴan sanda sun ci gaba da sintiri a yankin," in ji sanarwar.

Kazalika ta ce an sanar da gwamnati cewar ƴan fashi sun buɗe wa wasu mafarauta wuta a wani daji da ke yammacin ƙaramar hukumar Chikun.

A yanzu haka jami'an tsaro suna ci gaba da bincike don gano irin ɓarnar da ta faru. "Za mu sanar da al'umma abin da bincike ya gano," a cewar Mista Aruwan.

Gwamna Nasir El-Rufai ya roƙi al'ummomin garuruwan Tsohon Gaya da Sabon Gaya da sauran su da su kwantar da hankulansu kan ɓatan mafarautan.

Wannan layi ne

Sharhi

Wasu yankuna da dama na jihar Kaduna sun daɗe da yin bankwana da zaman lafiya saboda hare-haren ƴan fashi, sannan ita ma babbar hanyar Kaduna zuwa Abuja ta zama tarkon mutuwa ga matafiya.

A yanzu ƴan Najeriya da dama da ke bin hanyar sun ƙaurace mata inda suka gwammace su bi jirgin ƙasa ko kuma masu hali su bi na sama, maimakon su sadaukar da rayuwarsu wajen bin hanyar.

Bin hanyar na nufin ko dai a isa inda za a je lafiya ko kuma tsautsayi ya sa a ci karo da ƴan fashin inda za su shiga da mutum cikin daji a yi ta cinikinsa kamar goro, ba za a sake shi ba sai an biya kuɗin fansa.

Duk da cewa gwamnatoci na yawan nanata suna bakin ƙoƙarinsu don wanzar da zaman lafiya, har yanzu a bayyane yake cewa ba a ci galabar ƴan fashin ba balle a kammala daƙile su.

Ƙarin labaran da za ku so