Femi Adesina na shan suka kan kalaman da ya yi dangane da tsaro

Femi Adesina/Facebook

Asalin hoton, Femi Adesina/Facebook

Lokacin karatu: Minti 2

Masu amfani da shafukan sada zumunta a Najeriya na ci gaba da sukar sakataren watsen labaran shugaban Najeriya, Femi Adesina.

Wannan ya biyo bayan wata hira da Mista Femi ɗin ya yi da wani gidan talabijin na kasar inda ya ce ya kamata 'yan Najeriya su zama masu godiya ga Allah, a yanayin da suke ciki yanzu, yana cewa idan aka kwatanta da halin da Najeriya ta tsinci kanta a gwamnatin da ta gabace su.

"Akwai lokacin da bam ke tashi a kasar nan kullum sau hudu sau biyar, sai ka ce wasa, amma yanzu akan yi wata biyu zuwa uku babu abin da ya faru, ko wanne hali muka tsinci kanmu mu gode wa Allah.

"Ya kamata duk ƙanƙantar ci gaba da aka samu mu nuna godiya, kada mu riƙa mayar da hankali kawai kan abubuwan da suke faruwa marasa kyau," in ji Femi Adesina.

Waɗannan kalamai sun harzuƙa mutane da yawa a shafukan sada zumunta musamman na Twitter, ganin cewa ana ta fama da matsalar rashin tsaro da ta addabi wasu yankunan ƙasar.

Wasu sun riƙa yin raddi cikin yanayin shaguɓe, wasu kuma sun rika yin martani ne a cikin yanayin harzuƙa, daga cikin wadanda suka yi martanin akwai toshon ɗan Majalisar Dattijai na jihar Kaduna, Sanata Shehu Sani.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Shehu Sani ya ce "Godiya ga abokina Kanal Femi Adesina 'na rashin tashin bam'.

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2

Wannan ya ce "Femi Adesina ya bayar da kunya matuƙa saboda kalamansa, wannan hoton kuma ya nuna ƙarara kan abin da yake tunani".

Kauce wa X, 3
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 3

Wannan kuma cewa ya yi kalaman Femi Adesina kan tsaron Najeriya akwai siyasa a ciki. A cewarsa "Sun gaza wurin 'yan Najeriya. Su ci gaba da yin siyasa da rayukan jama'a".

Dalilin harzuƙar mutane

Femi Adesina/Facebook

Asalin hoton, Femi Adesina/Facebook

Ko a makon da ya gabata sai dai Femi Adesina ya sha suka a shafin Twitter bayan wata doguwar wasiƙaa da ya rubuta inda yake taya shugaban ƙasar murnar cika shekara 78 da haihuwa.

Babu daɗewa abokin aikin Femi Adesina, wato Malam Garba Shehu ya fito ya bayar da haƙuri game da wani bayani da ya yi kan yaran da aka sace a Katsina.

Malam Garba ya ce yara 10 ne suka yi saura a hannun 'yan bindigar da suka sace su.

Amma bayan sako yaran 344 sai ya yi wani sakon Twitter ya bayar da hakuri kan wannan bayani 'mara inganci' da ya bayar.

Kalaman na Garba Shehu na zuwa ne yayin da wasu 'yan ƙasar suke fushi da shi bayan kalamansa na cewa "Manoman da aka kashe a zabarmari ba su nemi izini ba suka je gona abin da yakai ga mtuwarsu".