Rashin tsaro: Mun san inda aka boye daliban Sakandiren Kankara - Masari
Gwamnan jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya Aminu Bello Masari ya ce sun san inda aka ɓoye ɗaliban makarantar sakandaren kimiyya ta maza ta Ƙanƙara da aka sace ranar Juma'ar da ta gabata.
Ya faɗi hakan ne a wata hira da ya yi da BBC Hausa ranar Laraba inda ya ce a halin yanzu suna da kyakkyawan yakini da bayanin inda yaran suke.
Gwamnan ya ce a yanzu haka bayanai sun nuna cewa yaran suna cikin dajin jihar Zamfara, "kuma ko ba dukkansu ba to mafi rinjayensu dai suna can wajen."
Ya ƙara da cewa a yanzu ƙoƙarin da gwamnati ke yi shi ne na a karɓo yaran ba tare da an yi amfani da bakin bindiga ba saboda kar a ji wa wsu rauni ko a kashe wasu bisa tsautsayi.
"A yanzu haka jami'an tsaro sun zagaye dukkan waɗannan wurare da ake zaton yaran suna can," in ji Masari.
Tun da farko dai gwamnatin jihar Katsinan ta ce yara 333 ne suke hannun ƴan bindigar da suka sace su ranar Juma'a da daddaren, a garin Ƙanƙaran da ke kusa da dajin Rugu da ya yi ƙaurin suna wajen zama maɓoyar ƴan fashin da suka addabi jihar Katsina da maƙwabtanta.
Amma wasu kafofin suna cewa yawan yaran da aka sace ɗin ya haura 600, duk da cewa wasu sun samu kuɓuta a ranar da abin ya faru.
Sai dai bayan da BBC ta tambayi gwamnan iya adadin da a yanzu suka san cewa suna hannun maharan, sai ya ce suna ci gaba da tattara bayanai daga iyayen da suke lunguna da saƙo da ake wahalar samunsu, "yanzu dai yaran za su kai daga 333 zuwa 400.
"Saboda akwai yaran da aka tabbatar da cewa suna makarantar kamar 867 a lokacin inda a yanzu 465 suke tare da iyayensu, wasu kuma suna hannun hukumar makaranta.
"Sannan ga sauran iyaye da ba za su iya zuwa Ƙanƙara ba an buɗe ofisoshi a kowace karamar hukuma ta jihar da za su iya zuwa su bayar da lambarsu da sunan ƴaƴansu, ta haka ne za mu iya tantance yawan yaran da suke hannun ƴan ta'addan."
Da wa gwamnatin Katsina ke tattaunawa tsakanin Boko Haram da ƴan fashin?

Asalin hoton, AFP
Kwana huɗu bayan sace ɗaliban ne sai shugaban ƙungiyar Boko Haram da ke arewa maso gabashin Najeriyar Abubakar Shekau ya fitar da wani saƙon murya yana iƙirarin sace yaran.
Al'amarin ya sanya ruɗani a zuƙatan mutane ganin cewa Boko Haram na ayyukanta ne a arewa maso gabashin ƙasar yayin da wannan sata kuma aka yi a arewa maso yamma.
Sai dai masu sharhi na cewa ba abin mamaki ba ne don ƙungiyar ce ta yi ƙaurin suna wajen sace ƴan makaranta kamar yadda ya faru a Chibok da Dapchi. Sannan kuma a kwanakin baya Shekau ɗin ya ce ƙungiyarsa na kai wasu hare-hare yankin arewa maso yamman.
Amma a hirar BBC da Gwamna Masarin cewa ya yi su dai a nasu ɓangaren masu garkuwa da mutane suka sani da wannan aika-aika. "Su muka sani, kuma su ne muke da yaƙinin cewa da su ake ta batun tattaunawar nan.
"Maganar ƴan Boko Haram idan maganar da ake yi da su ta kai ga sun gwada cewa akwai wasu daga waje to a lokacin ne tunanin cewa Boko Haram na da hannu na kai tsaye zai zo. Amma mun sani an bayar da rahoto cewa Boko Haram na da alaƙa da wasu ƴan ta'addan nan," a cewarsa.
Nawa ɓarayin ke nema na kuɗin fansa?
Kamar yadda aka sani tattaunawa da masu satar mutane na nufin ciniki kan kuɗin fansar da suke buƙata, amma a wannan lamarin Gwamna Aminu Masari ya ce ba wani wanda ya nemi kuɗin fansa.
"Abin da muka sani shi ne cikin yaran da suka sace akwai ɗan malamin makarantar wanda suka yi amfani da wayarsa suka kira mahaifinsa suka ce ba sa so ana tura musu jirage.
"Su kuɗi kawai suke so a ba su, amma daga nan ba su kara kira ba, wayar kuma ba ta ƙara aiki ba," kamar yadda Gwamna Masari ya bayyana.














