Da gaske ƴan jarida da ƴan siyasa na son rusa gwamnatin Buhari?

Masana a Najeriya sun fara tsokaci dangane da iƙirarin fadar shugaban Najeriya na cewa wasu yan siyasa na haɗa kai da jaridun internet don baƙanta gwamnatin Muhammadu Buhari, da kuma nuna cewa ba shugaban ne ke jagorancin ƙasar ba.

A cikin wata sanarwa da mai taimaka wa shugaban kasar kan harkokin watsa labarai Mista Femi Adesina ya fitar ranar Laraba, ya ce shirin da wasu ƴan siyasa "Marasa kishin ƙasa" suka yi shi ne na bai wa jaridun kudi don su riƙa watsa labaran ƙarya da zummar cimma wata manufa ta siyasa.

Ya kara da cewa tuni wasu jaridun suka amince da wannan tayi, har ma sun fara abin da aka nemi su yi na ƙirƙirar labaran ƙarya da kuma shafa wa Shugaba Muhammadu Buhari baƙin fenti.

A cewa fadar shugaban kasar dai ta fahimci cewa masu shiryawa shugaban kasar wannan tuggu, na yi ne saboda dalilai na cimma bukatun siyasa.

Dakta Abubakar Kari, wani mai fashin baki kan al'amuran yau da kullum a Najeriya ya ce ba sabon abu bane gwamnati ta yi zargin cewa ana shirya mata kutungwila don ɓata sunanta, ko ma nuna ba ta yin abin da ya kamata.

Ya ce gwamnatocin da suka gabata ma sun yi irin wannan, saboda haka abu ne da ya riga ya zama jiki ga yan siyasar Najeriya.

A cewarsa, idan har gwamnati ba ta son suka, to kamata ya yi ta toshe duk wata ƙofa da za a soke ta a kanta, idan ta yi haka ta lulluɓawa kanta bargon kariya.

"Adawa da kuma dimokraɗiyya na nufin abokin hamayyarka ya soki inda ya ga aibunka, don haka idan gwamnati ba ta son shan suka sai ta bai wa maraɗa kunya," in ji Dakta Kari.

Abin da ke jawo zargin

Dangane da zargin da fadar shugaban ta yi na cewa ana son nunawa duniya cewa ba Buhari ba ne ke jagoranci, masanin ya ce a yanzu mutane da dama na ƙara yarda da ikirarin da wasu mutane suka yi a baya na cewa ba Buharin ne a fadar shugaban kasa ba, ko bai san halin da kasar ke ciki ba, ko kuma wasu ne ke tafiyar da harkokin ƙasar a ɓoye.

"Dalili kuwa shi ne rashin ganinsa a bainar jama'a, da kuma rashin yin magana a duk sa'ad da bukatar hakan ta taso.

Masanin ya kara da cewa ɓoye kansa da shugaban kasar ke yi ya sa an kasa gane inda gwamnatinsa ta sanya gaba, sannan ya kara karfafa kace nace da zargi a tsakanin jama'a.

Adesina dai ya ƙara da cewa ga dukkanin wadanda ke tababar irin ayyukan da gwamnatin ke yi wa jama'a, yana iya kallon manyan ayyukan da ta samar, kama daga kan gadoji da filayen jiragen sama, da kuma inganta fannin noma.

To sai dai wani abu da masu magana da yawun shugaban suka ce ba zai gushe yana yi ba shi ne yaƙi da cin hanci da rashawa, wanda ya zamewa kasar ƙarfen ƙafa.