Emmanuel Macron: Shugaban Faransa ya kamu da cutar korona

Asalin hoton, EPA
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya kamu da cutar korona.
Shugaban mai shekaru 42 yanzu zai keɓe kansa har tsawon kwanaki bakwai, kamar yadda fadar Elysée ta fada a cikin wata sanarwa.
Har yanzu yana ci gaba da ayyukansa a matsayinsa na shugaban ƙasa, in ji wani jami'i.
Shugaban ƙungiyar Tarayyar Turai Charles Michel da Firai ministan Spaniya Pedro Sánchez duk sun keɓe kansu bayan sun yi mu'amala da Mista Macron a ranar Litinin.
A makon nan ne Faransa ta janye dokar kullen da ta kafa don yaki da cutar.
Zuwa yanzu mutane miliyan biyu ne suka kamu da cutar a kasar tun bayan bullarta.
Su wa Macron ya yi hulɗa da su ?
Elysée ta ce yau ne aka gano cewa shugaban na ɗauke da cutar.
Bayanin ya ƙara da cewa an gano hakan ne bayan "gwajin da aka gudanar bayan ganin alamunta tattare da shugaban.
Har yanzu ba a san yadda Mista Macron ya kamu da cutar ba amma ofishinsa ya ce yana gano duk waɗanda ya yi mu'amala da su a kwanakin baya.
Firai minista Jean Castex, mai shekaru 55, da kakakin majalisar Richard Ferrand, mai shekaru 58, duk sun kebe kansu kamar yadda ofisoshinsu suka tabbatar.

Asalin hoton, Reuters
Pedro Sanchez mai shekara 48 da Charles Michael mai shekara 44 duk sun killace kansu, bayan wata ganawa da shugaba Macron a ranar litinin.
Ofishin Firai ministan na Spaniya ya ce za a yi wa shugaban gwaji ba tare da bata wani lokaci ba, sannan zai bi dokar killace kansa kamar yaddda doka ta tanada.
Shima Firai ministan Portugal Antonio Costa ya soke ziyarar da ya shirya kaiwa wasu ƙasashe, sannan yana jiran sakamakonsa, bayan da shuma ya ci abincin dare da shugaba Macron a ranar Laraba.
Ana tunanin shugaban zai iya zama silar yadawa mutane da dama cutar a ranar Litinin, kamar yadda wani jami'in EU ya shaida wa BBC.
Domin ya halarci taron shugabannin kasashen turai na yini biyu da aka gudanar a ranar Alhamis.

Asalin hoton, EPA
An dauki dukkan matakan kariya a wajen taron na makon jiya kuma majalisar ba ta fadi cewa wani daga cikin mahalarta taron ya kamu da cutar korona ba, a cewar wata majiya.
Wata mai magana da yawun Mr Macron ta ce an soke duk wasu tafiye-tafiyen da zai yi, ciki har da ziyarar da zai kai Lebanon ranar 22 ga watan Disamba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X

Hukumar magunguna ta tarayyar turai (EMA) na shirin zama a ranar Litinin domin duba riga-kafin da aka soma amfani da shi a wasu kasashe.
Shugaba Macron na cikin shugabannin kasashen duniya da suka kamu da cutar korona,
Firaiministan Burtaniya Boris Johnson shima ya kamu da cutar, harma ya kare a sashen bada kulawar gaggawa na asibiti, sakamakon yadda cutar ta yi tasiri a jikinsa.

Wadanne shugabanni ne suka kamu da cutar ?

Asalin hoton, Getty Images
• Firai minista Ambrose Dlamini na Eswatini ya mutu a ranar Litinin, makonni huɗu bayan kamuwa da cutar.
• Shugaban Amurka Donald Trump ya kamu da cutar a watan Oktoba.
• Shugaban ƙasar Poland Andrzej Duda ya kamu da cutar a watan Oktoba kuma ya kebe kansa.
• Shugaban Algeria Abdelmadjid Tebboune ya kwashe watanni biyu yana jinya a kasar Jamus bayan kamuwa da cutar a watan Oktoba , a makon da ya gabata ya fito a bidiyo a karon farko tun bayan da aka tabbatar yana dauke da cutar, yana mai cewa yana fatan komawa Algeriya ba da jimawa ba
• Shugaban Guatemala Alejandro Giammattei ya kamu da cutar a watan Satumba.
• Jair Bolsonaro na Brazil ya kamu da korona a watan Yuli kuma ya kwashe sama da makonni biyu a kebe.
• A watan Yuni, shugaban Burundi mai barin gado Pierre Nkurunziza ya mutu sakamakon rashin lafiya da ake zargin korona ce.
• Firai ministan Rasha Mikhail Mishustin ya kamu da cutar a watan Afrilu kuma an kai shi sashen bada kulawar gaggawa.
• Firai ministan Burtaniya Boris Johnson ya kamu da cutar korona a watan Maris.











