Ɗan ƙasar Faransa zai sha ɗauri kan harbe zakaran da ya dame shi da cara

Zakara

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Wannan ita ce taƙaddamar da ta shafi zakara da ta mamaye kafafen yaɗa labarai a baya-bayan nan a Faransa (wannan ba ainihin hoton Mercel ba ne)

An yanke wa wani mutum a ƙasar Faransa hukuncin ɗaurin shekara biyar sakamakon samunsa da laifin harbe wani zakara tare tsire shi da wani ƙarfe saboda ya dame shi da cara.

Zakaran, mai suna Marcel wanda ya fito daga jihar Ardèche, maƙwabcinsa ne ya harbe shi a watan Mayu bayan carar da yake yi ta fusata shi.

Sebastien Verney, mai zakaran, ya rubuta takaradar neman a yi wa zakaran nasa adalci. Kuma tuni kusan mutane dubu ɗari ɗaya suka rattaba hannu a kan takardar.

An kuma samu maƙwabcin nasa da aikata laifin yi wa dabba mugunta da sauran laifuka.

Baya ga hukuncin da aka yanke masa, an kuma ci tararshi €300 tare da dakatar da shi daga riƙe duk wani maƙami tsawon shekara uku.

"Wannan ba zai taɓa gyara abin da ya aikata ba," Mista Verney ya shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP.

A takardar ƙarar da ya rubuta, ya yi magana kan "mummunan abin baƙin ciki" da ya faɗa wa iyalan, yayin da ya yi kira a kan cewa kada ƙauyuka su zama wurin ajiyar kayan tarihi.

"Su waye za su sake faɗawa cikin wannan barazana? Tattabarun da ke kuka, girbin alkama, noman tumatir, kukan jaki, ƙarar ƙararrawar agogo ko kuma kiwon shanu?"

Wannan ita ce taƙaddamar da ta shafi zakara da ta mamaye kafafen yaɗa labarai a baya-bayan nan a ƙasar Faransa.

A shekarar da ta wuce ma, wata kotu a Faransa ta yanke hukuncin da ya goyi bayan wani mai zakara, bayan da maƙwabtansa suka kai koken cewa yana damunsu da cara da sassafe.

A cikin watan Yuni ne dai zakaran mai suna Maurice, ya mutu yana da shekara shida.

Me yiwuwa za ku so ku ga wannan:

Bayanan bidiyo, Carar zakara mai karfi tare da karkada fukafukai a yankin Robin Hood Bay