Omah Lay Uganda: Najeriya na bakin kokarinta wajen ganin ta karbo Omah Lay, da Tems da aka tsare a Uganda - Abike Dabiri

Omah Lay Uganda: Nigeria dey do everi to free Omah Lay, Tems arrest in Uganda - Abike Dabiri

Asalin hoton, Twitter / IsimaOdeh

Lokacin karatu: Minti 2

Wata babbar jami'a a gwamnatin Najeriya ta ce ofishin jakadancin kasar da ke Uganda na iya bakin kokarinsa domin ganin ya karbo mawakan Omah Lay da aka tsare a kasar ranar Lahadi.

Amma kuma mahukuntan kasar ta Uganda sun ce dole ne a bi dokarsu, in ji Abike Dabiri, shugabar hukumar lura da 'yan Najeriya mazauna kasashen waje [NIDCOM].

Ta kara da cewa, ministan harkokin kasashen waje Geoffrey Onyeama wanda shi ma ya shiga cikin al'amarin tare da hukumar ta NIDCOM suna tattaunawa da lauyoyinsu.

'Yan sandan kasar ta Uganda sun cafke Omah Lay da Tems a bisa zargin karya dokokin cutar korona.

Omah Lay da Tems

Asalin hoton, Odas

Mahukuntan sun saka wa Omah Lay da Tems ankwa tare da tsare su a gidan yari kan zargin karya dokokin na cutar ta korona.

Stanley Omah Didia da aka fi sani da Omah Lay, da Temilade Openyi da aka fi sani da Tems da kuma Muyiwa Awoniyi sun bayyana a gaban kotu ranar Litinin 14 ga watan Disamba, inda ake tuhumarsu kan zargin "nuna halin ko in kula kan abinda ka iya yada cutar".

'Yan sandan kasar ta Uganda sun kuma tabbatar da tuhumar wasu 'yan kasar hudu tare da 'yan Najeriyar.

Kauce wa X, 1
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 1

Wannan lamari ya ja hankalin 'yan Najeriya musamman wadanda ke amfani da shafukan sada zumunta.

Galibin wadanda suka yi tsokaci a kan batun sun soki mawakan bisa kin yin biyayya ga dokokin kasar ta Uganda.

Sai dai wasu sun rika fafutukar ganin an saki mawakan biyu.

Daya daga cikinsu shi ne tsohon dan majalisar dattawan Najeriya Ben Bruce wanda ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta kara kaimi wurin ganin an sake su kuma ta tabbatar "ba su yi Kirsimeti a gidan yari ba."

Kauce wa X, 2
Ya kamata a bar bayanan X?

Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.

Gargadi: Ana iya samun talla wanda ba na BBC ba ne

Karshen labarin da aka sa a X, 2