Jihar Katsina: 'Yan bindiga sun 'sace ɗalibai da dama' a makarantar sakandaren Kankara

Asalin hoton, Gali Kankara
Har yanzu wasu iyayen ɗalibai na jiran tsammani a harabar makarantar sakandare ta GSSS Ƙanƙara, inda wasu 'yan bindiga suka kai hari a daren Juma'a tare da yin awon gaba da ɗaliban da dama.
BBC ta samu rahotannin cewa Gwamnan Katsina Aminu Bello Masari ya je makarantar, inda ya yi yunƙurin yi wa iyayen yaran jawabi amma jama'a suka yi masa ihu, har sai da aka harba hayaƙi mai sa hawaye kafin tawagar gwamnan ta iya barin wurin.
Wani wanda lamarin ya faru a kan idonsa ya bayyana cewa har yanzu akwai iyayen da ba su ga yaransu ba kuma shi ma yana tare da wani daga cikinsu, inda yake taya shi neman ɗansa.
Rahotanni sun ce 'yan bindigar sun kai harin ne a makarantar sakandaren ta maza zalla da ke garin Ƙanƙara da misalin ƙarfe 11:00 na dare.
Har zuwa yanzu babu tabbacin adadin ɗaliban da suka ɓata bayan harin amma wasu rahotanni na cewa kusan 400 ne ba a gani ba bayan an lissafa waɗanda suke nan.

Asalin hoton, Gali Kankara
Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar wa BBC kai harin amma ta ce ba ta da bayanai kan sace ɗaliban.
Mai magana da yawun rundunar, DSP Gambo Isa, ya ce tuni aka gano ɗalibai fiye da 200 da suka tarwatse suka shiga cikin daji a lokacin da 'yan bindigar suka auka wa makarantar tasu.
Ya ƙara da cewa an yi ba-ta-kashi tsakanin 'yan bindigar da 'yan sanda lamarin da ya kai ga "harbin ɗan sanda ɗaya amma bai mutu ba."
A cewarsa, an tura ƙarin 'yan sanda domin su far wa 'yan bindigar yana mai cewa kawo yanzu suna ci gaba da ƙirga ɗaliban da suka koma makarantar daga daji a kuma waɗanda ba su dawo ba domin sanin ainihin yawan waɗanda aka sace.

Sai dai wani ganau ya shaida wa BBC cewa an sace ɗalibai da dama a harin da 'yan bindigar suka kai.
Mutumin, wanda ba ya so mu ambaci sunansa, ya ƙara da cewa: "A gabana 'yan bindigar suka wuce suna harbe-harbe suka shiga makarantar kuma sun sace ɗalibai da dama. Tun da yamma muka samu labarin cewa za su kawo hari kuma mun shaida wa jami'an tsaro amma ba a ɗauki mataki ba."











