Hotunan kufayi da suka ci gasar duniya

Wani kantin gahawa, Abkhazia.

Asalin hoton, Jonk

1px transparent line

Wasu hotuna da aka dauka a wasu kufayi masu kyawun yanayi sun lashe gasar hotuna ta 2020.

Jerin hotunan wandanda wani mai daukar hoto na Faransa Jonathan Jimenez ya dauka sun hadar da wani shagon sayar da gahawa dake Abkhazia, da wani Otal a Portugal da kuma wani ninkaya a Italiya.

An zakulo su ne daga ire-irensu 2,600.

Marissa Roth, wanda ta jagoranci gasar ta ce sun zabi aikin Jonahan ne saboda tsabagen kwarewar da ya nuna da sakon da suke kunshe da su.

A cewarta, hotunan na nuna alakar dake tsakanin bil'adama da yanayi.

Hukumar kula da dazukan Indiya ta zabi wadanda suka lashe gasar a rukuni shida.

An shirya gasar ne da manufar baje kolin mafi kyawun muhalli, da kuma aniyar bunkasa muhawara dangane da duniya da abin da ke cikinta.

Wani mutumi da ke shan sigari a Liangshan Yi Autonomous dake China

Asalin hoton, Yanrong Guo

1px transparent line

Yanrong Guo ta ci gasar da hotonta mai suna Miss, dake nuna wani mutumi a tsaye a Liangshan yana zukar sigari,.

Sahun wata tarakta kenan a wata gona a Spaniya

Asalin hoton, Yi Sun

1px transparent line

Yi Sun ya lashe gasar bangaren yanayi, da hotonsa mai taken Dryland Farming, Study 7, wanda ke nuna sahun tarakta yayin da take ratsawa ta cikin wata gona a Spaniya.

Kututturen icen wata bishiya

Asalin hoton, Charles Xelot

1px transparent line

Charles Xelot ya lashe gasar bangaren yanayin dazuka dake nuna kututturen icen wata bishiya bayan shekara biyu da samun gobarar daji da mutane suka haddasa.

Wani mutum dake tsaye a tsakiyar ruwa a Venice, dake Italiya.

Asalin hoton, Joe Habben

1px transparent line

Joe Habben ya lashe gasar ta bangaren sauyin yanayi, da wani hotonsa dake nuna cutarwar ruwa mai yawa a Venice.

A bangaren bidiyon da yafi kowanne agasar kuwa Sean Gallagher ne ya lashe gasar, da bidiyonsa dake nuna illar sare dazuka a Cambodia.

An samu dukkan wadannan hotuna daga : Royal Geographical Society