Zaɓen Ghana: Nana Akufo-Addo ya lashe zaɓen ƙasar

Hukumar zaɓen Ghana ta sanar da cewa shugaban ƙasar mai ci Nana Akufo-Addo ne ya lashe zaɓen ƙasar inda ya yi nasara a kan babban abokin hamayyarsa tsohon Shugaba John Dramani Mahama.

Shugaba Nana Akufo Addo ya yi nasara da kashi 50.8 cikin 100 a cewar shugabar hukumar zaɓen Jean Mensa. Alƙaluman sun nuna cewa Nana Akufo-Addo na jam'iyyar NPP ya samu ƙuri'a 6,730,413.

Shi kuma John Dramani Mahama na jam'iyyar NDC ya samu ƙuri'a 6,214,889 wato kashi 47.36 cikin 100.

Fiye da mutum miliyan 17 ne suka kaɗa kuri'unsu a zaben.

Zaɓen shi ne na farko da Ghana ta yi da na'ura, wani abu da ƴan ƙasar za su yi alfahari da shi.

Akufo-Addo zai ci gaba da shugabancin ƙsar a karo na biyu.

Ya zuwa ranar Laraba da yamma, an bayyana sakamakon zaɓen larduna 15 kamar haka:

  • Upper West: NPP: 121,230 - NDC: 238,972
  • North East: NPP: 122,742 - NDC:112,306
  • Bono East: NPP: 153,341 - NDC: 213,694
  • Oti: NPP: 103,865 - NDC: 181,021
  • Volta: NPP: 100,481 - NDC: 606,508
  • Ahafo: NPP: 145,584 - NDC: 116,485
  • Ashanti: NPP 1,795, 824 -NDC 653, 149
  • Savanna: NDC 144, 244 -NPP 80,60
  • Upper East: NDC 335, 502 -NPP 170, 340
  • Western Region: NPP 439, 724 -NDC 398, 549
  • Central: NPP: 613,804 - NDC: 538,829
  • Bono Region: NPP: 292, 604 - NDC: 203,329
  • Eastern Region: NPP: 752,061 - NDC: 470,999
  • Western North Region: NPP: 175,240 - NDC: 196,556
  • Northern Region: NDC: 476,550 - NPP: 409,963