Abin da ya sa Dattawan Arewa suke so Buhari ya sauka daga mulki

Asalin hoton, Channels Tv
Ƙungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ta ce ta yi kira ga shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya sauka daga mulki ne saboda ya gaza kare rayukan al'ummar ƙasar.
Mai magana da yawun ƙungiyar Dr Hakeem Baba-Ahmed ya shaida wa BBC cewa sun ɗauki wannan matsaya ne sakamakon yankan ragon da mayaƙan Boko Haram suka yi wa mutum fiye da 40 a Zabarmari da ke jihar Borno.
"Mun sha yi wa shugaban ƙasa hannunka mai-sanda, har ta kai ƙiri-ƙiri muna cewa 'shugaban ƙasa, ka rantse za ka yi shugabancin Najeriya, ka rantse da AlƘur'ani za ka kare mu, yanzu shekara biyar ko shida ba mu ga alama wannan alƙawari naka ya cika ba sai ma taɓarɓarewa da al'amura suka yi," in ji Dr Ahmed.
A cewarsa, a ƙasashen da suka ci gaba idan shugaba ya gaza cika alƙawuran da ya yi ya kamata ya sauka.
Ya ƙara da cewa sun shafe lokaci mai tsawo suna tattaunawa kafin su yi kira ga shugaban ya sauka daga mulki, yana mai cewa "kuma ya gazan ne shi ya sa muka yi wannan kira, ba sharri muke yi masa ba."
"Rayuwa ba ta da amfani a ƙarkashin mulkin shugabancin Buhari, kashe mu ake yi daga ko ina - daga Sokoto zuwa Borno, daga Taraba zuwa Naija. Sannan kuma 'yan kudancin Najeriya," a cewar kakakin ƙungiyar Dattawan Arewacin Najeriya.
Wannan kira da ƙungiyar Dattawan Arewacin Najeriya ya zo daidai da irin wanda 'yan ƙasar da dama suke yi ga shugaban ƙasar, ciki har da malaman addinin Musulunci.
Arewacin ƙasar na cikin hali na rashin tsaro inda kusan kullum sai an kashe mutane ko an yi garkuwa da su a yankin. Magance matsalar tsaron na ɗaya daga cikin manyan alƙawuran da shugaban ya yi a lokacin yaƙin neman zaɓe a 2015, lokacin da aka zaɓe shi a karon farko.
Amma 'yan ƙasar da dama na ganin gwamnatinsa ta gaza ta wannan fuska.
'Yan bindiga da ɓarayin shanu da masu garkuwa da mutane, sun addabi jihohin da ke arewa maso yamma, yayin da Boko Haram ke ci gaba da ɓarna a arewa maso gabashin ƙasar.
Haka zalika ana samun matsalar garkuwa da mutane a sauran sassan ƙasar.











