Ana ce-ce-ku-ce kan batun gwajin lafiyar ƙwaƙwalwar Buhari

Asalin hoton, AFP
Tsohuwar ministar ilimi kuma tsohuwar 'yar takarar shugabar ƙasa a Najeriya, Oby Ezekwesili, ta yi kira da a duba lafiyar ƙwaƙwalwa da kuma lafiyar jikin Shugaba Muhammadu Buhari.
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ya kamata 'yan Najeriya su yi ƙoƙari wajen tabbatar da an kafa wani kwamiti mai zaman kansa na musamman domin duba lafiyar shugaban ƙasar.
Ta bayyana cewa halin da Najeriya ke ciki ya wuce a zauna a zura ido ana kallo ta lalace.
Ta kuma bayyana cewa; "A matsayina na 'yar ƙasa da ta damu, ina buƙatar a kafa kwamitin binciken lafiyar Shugaba Buhari, domin ba mu amince likitan Fadar Shugaban Ƙasa zai ba mu ingantattun bayanai ba".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Me Fadar Shugaban Ƙasa ta ce?
Mai magana da yawun shugaban Najeriya Malam Garba Shehu, ya shaida wa BBC cewa ba za su ce komai ba kan wannan lamarin domin sama da shekara shida, duk abin da Oby Ezekwesili ta ce ba su mayar da martani ba.
Ya kuma tabbatar da cewa shi ma ya ga ana yaɗa wannan labari a shafukan sada zumunta, amma duk da haka ba zai ce komai ba.
Me mutane ke cewa?
Wannan kira da tsohuwar ministar ta yi ya raba kan 'yan Najeriya inda wasu suka goyi bayanta yayin da wasu suka soki kiran da ta yi. Muhawarar ta fi zafi a shafukan intanet.
Wannan cewa ya yi ya kamata a duba wannan batun na Oby domin a cewarsa, bai kamata a ce ana kashe jama'a shugaban yana shiru ba.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
A cewar wannan mai amfani da Twitter, wannan lamari duk hassada ce irin ta 'yan siyasa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Me ya janyo ce-ce-ku-ce?
'Yan Najeriya da dama sun fusata sakamakon matsalar tsaro da ta ƙi ci ta ƙi cinyewa a ƙasar. Haka kuma wasu 'yan ƙasar na zargin cewa shugaban ya kasa ɗaukar ƙwaƙƙwaran mataki da zai kawo ƙarshen matsalar yayin da wasu ke ganin take-takensa na nuna bai ma san halin da ake ciki ba.
Arewacin kasar na cikin hali na rashin tsaro inda kusan kullum sai an kashe mutane ko an yi garkuwa da su a yankin. Magance matsalar tsaron na daya daga cikin manyan alkawuran da shugaban ya yi a lokacin yakin neman zabe a 2015, lokacin da aka zabe shi a karon farko. Amma 'yan kasar da dama na ganin gwamnatinsa ta gaza ta wannan fuska.
'Yan bindiga da ɓarayin shanu da masu garkuwa da mutane, sun addabi jihohin da ke arewa maso yamma, yayin da Boko Haram ke ci gaba da ɓarna a arewa maso gabashin ƙasar. Haka zalika ana samun matsalar garkuwa da mutane a sauran sassan ƙasar.
Hakan ya ja 'yan ƙasar ke ta kira ga shugaba Buhari da ya sauya manyan hafsoshin tsaro, amma ga alama kawo yanzu ya yi biris da kiran duk da cewa Majalisar Dokoki ta Tarrayar Najeriya tana cikin masu buƙatar ya yi hakan.