Rashin tsaro: 'Muna so Buhari ya sauka daga mulkin Najeriya'

Asalin hoton, Presidency
'Yan Najeriya da dama musamman a shafukan sada zumunta sun fusata, inda suke tattaunawa kan maudu'ai daban-daban inda suke nuna ɓacin ransu da kuma kira ga Shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya sauka.
'Yan ƙasar dai dai sun fusata ne tun bayan da wasu da ake zargin 'yan Boko Haram ne suka kashe manoma 43, inda daga baya Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayyana cewa mutum 110 aka kashe.
Hakan ya ja 'yan Najeriya suka fitar da mau'du'ai daban-daban waɗanda suka haɗa da #BuhariMustGo da #BuhariResignNow, wanda hakan ke nufin Buhari ya sauka daga mulki, akwai kuma mau'du'in #SackTheServiceChiefs wato a sallami shugabannin tsaron ƙasar.
Haka kuma akwai maudu'in da aka fito da shi na #EndNaijaKillings wato kawo ƙarshen kashe-kashen Najeriya, da kuma #ZabarmariMassacre wanda maudu'i ne da ke jaje ga manoman na garin Zabarmari da aka kashe a Bornon.
Duka waɗannan mau'du'an da ake tattaunawa sun samu karɓuwa a shafin Twitter inda mutane ke ci gaba da yaɗa su da rarraba su, kuma akasarin mutanen da ke waɗannan ƙorafe-ƙorafen suna nuna gazawar shugaban ƙasar da kuma neman ya sauka daga kan mulki.
Sai dai tun bayan wannan mummunan kisan da aka yi wa manoma a Borno, tuni mai magana da yawun shugaban ƙasar Garba Shehu, ya fitar da sanarwa inda ya bayyana cewa Shugaba Buhari ya nuna damuwarsa matuƙa kan lamarin kuma yana bai wa sojoji gudunmawa kuma zai ci gaba da ba su gudunmawar domin samar da tsaro.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 1
Me 'yan Najeriya je cewa a Tuwita?
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 2
Wannan cewa ya yi "ba ma so Buhari ya sallami shugabannin tsaro, so muke ya sauka daga mulki".
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 3
Wannan kuma cewa ya yi ya kamata a yi wani abu. A cewarsa, wani babban bala'i na nan tafe, ya kuma buƙaci shugaban ƙasar da ya sauka daga mulkinsa.
Wannan labari ne na dauke da bayanai da X suka bayar. Muna neman amincewarku kafin mu dora muka, saboda nuna iya dauke da wasu bayanai da aka iya adanawa. Watakila kana za ka so ka karanta X da tsarin bayanan da za a adana da da tsarin sirri kafin ka amince. Idan kana son ganin wannan bayani ka zabi ‘amince sannan ka ci gaba’.
Karshen labarin da aka sa a X, 4
Wannan kuma ta nuna damuwa ne kan manoman da aka kashe inda ta ce mutanen Najeriyar suna cikin rashin tsaro. Ta yi zargin cewa Shugaba Muhammadu Buhari bai damu da su ba, ta kuma ce ba za su ci gaba da ɗaukar wannan abin da ke faruwa ba.
Haka kuma, ita ma ta buƙaci Shugaba Buharin da ya sauka.
Tura ta kai bango
Ba wannan ne karo na farko da ƴan Najeriya suka fara kiraye-kiraye ga Shugaba Buhari da ya sauka a kan mulki ba.
A cikin wannan shekarar a wani lokaci da ƴan bindiga suka addabi jihohin Zamfara da Katsina da kai hare-hare, ƴan ƙasar sun yi ta kira ga Buharin da ya sauka, amma shugaban ko uffan bai ce ba.
Sannan a nan baya-bayan nan ma an ga yadda ƴan kudancin ƙasar suka dinga kira ga Buharin cewa sai ya sauka daga mulkin saboda ya gaza kare rayukan ƴan ƙasa daga kashe su da ƴan sandan rundunar Sars ke yi.
Ba waɗannan ne kawai lokutan da aka buƙaci shugaban ya sauka ba, an yi hakan ya fi sau shurin masaki.