Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Mohsen Fakhrizadeh: Iran na zargin Isra'ila da kashe mata masanin kimiyyar nukiliya
Shugaban Iran ya zargi Isra'ila da kisan babban ƙwararre kan shirin nukiliyarta ranar Juma'a, tana mai cewa ba za ta taɓa ja da baya ba game da shirin.
Hassan Rouhani ya kuma ce ƙasarsa za ta yi ramuwar gayya game da kisan Mohsen Fakhrizadeh a lokacin da ta zaɓa.
An kashe Fakhrizadeh ne a wani harin kwanton-ɓauna da 'yan bindiga suka yi a kan motarsa a garin Absard da ke gabashin birnin Tehran.
Isra'ila ba ta ce komai ba game da batun zuwa yanzu, amma ta taɓa zarginsa da jagorantar wani shirin ƙera makamin nukiliya a baya.
Fakhrizadeh ne mafi shahara a cikin masana kimiyyar nukiliya na Iran, wanda ya jagoranci shirin a ƙarƙashin ma'aikatar tsaro.
Kisan nasa ka iya ƙara rura wutar rikici kan shirin ƙera nukiliya da Iran ke yi tsakaninta da Amurka da sauran ƙawayenta da suka ƙulla yarjejeniya.
Mene ne ya faru?
A sanarwar da ta fitar ranar Juma'a, ma'aikatar tsaron Iran ta ce " Wasu 'yan ta'adda dauke da makamai sun hari motar da ke dauke da Mohsen Fakhrizadeh, shugaban fannin bincike da tsare-tsare na ma'aikatar."
"Bayan dauki ba dadi tsakanin 'yan ta'addan da masu tsaron lafiyarsa, Mr Fakhrizadeh ya samu munanan raunuka inda aka garzaya da shi asibiti."
"Abin takaici shi ne, yunkurin likitoci na ceto rayuwarsa ya ci tura kuma a mintuna kadan da suka wuce ya mutu."
Kafafen watsa labaran Iran sun ruwaito cewa maharan sun bude wuta kan motar masanin kimiyyar nukiliyar.
Tun da farko rahotanni sun ce an samu fashewar wani abu a garin Absard, abin da ganau suka ce ya yi sanadin mutuwar "mutum uku ko hudu, wadanda su ka ce 'yan ta'adda ne".