Ali Ƙwara: Abu biyar kan fitaccen mai kama barayin da ya rasu

Ali Kwara

Asalin hoton, Family

Bayanan hoto, Ali Ƙwara ya rasu ranar Juma'a a Abuja bayan fama da rashin lafiya

An yi jana'izar fitaccen mafaraucin nan kuma mai kama barayi, Alhaji Ali Kwara a garin Azare a ranar Asabar.

Ali Kwara ya rasu ne a wani asibiti a Abuja ranar Juma'a bayan ya sha fama da rashin lafiya.

Manyan mutane daga sassan Najeriya daban-daban ne suka halarci jana'izar tasa.

Shugaban Najeriya Muhammadu Bubari ya aika sakon ta'aziyyarsa ga iyalan marigayin da al'ummar Jihar Bauchi kan "wannan babban rashi da aka yi."

Fadar shugaban ƙasar ce ta bayar da jirgin saman da aka ɗauki gawar marigayin daga Abuja zuwa filin jirgin sama na Dutse, inda daga can aka wuce da shi mahaifarsa ta Azare.

Ga wasu abubuwa biyar da watakila ba ku sani ba game da marigayin:

Dan asalin ƙasar Yemen ne

Ali Kwara

Asalin hoton, Family

Alhaji Ali Kwara dan asalin kasar Yemen ne. Mahaifinsa Alhaji Muhammad Kwara ya shigo Najeriya a lokacin yana da shekara 18 inda ya ya da zango a garin Azare na jihar Bauchi.

Ya auri Hajiya Safiyya wadda ita kuma 'yar asalin kasar Libiya ce.

Sun haifi 'ya'ya bakwai da suka haɗa da Hajiya Maryam da Alhaji Ali Ƙwara da Usman da Abba da Fatima da Hashim da Abdulhamid da kuma Ahmad.

An haifi Ali a shekarar 1958 a wata unguwa mai suna Garin Arab a cikin Azare.

Garin Arab nan ne inda dangin Ali fararen fata suka mamaye, shi ya sa aka sa mata wannan sunan.

Ali Ƙwara ya yi karatunsa na firamare da sakandare duk a garin Azare.

Sana'ar fata da gyaɗa

Ali Ƙwara ya shahara a wajen sana'ar sayen fatun dabbobi tare da kI su kamfani a sarrafa.

Sannan kuma ya yi sana'ar gyaɗa sosai inda har yake fitar da ita wasu ƙasashen.

Ya gaji waɗannan sana'o'i ne daga mahaifinsa wanda yake yin su tun zuwansa Najeriya.

"Duk wanda ya san Ali sosai to ya san shi da waɗannan nan sana'o'i," in ji ɗan'uwansa Alhaji Abba.

Farauta

Ali Ƙwara ya yi fice sosai a matsayin fitaccen mafarauci a Najeriya.

Makusantan Ali Ƙwara sun ce tun yana yaro yake sha'awar farauta kuma yake yin ta.

Ɗan uwansa Abba ya ce "mutum me marar tsoro mai dakakkiyar zuciya.

"Babu yankin da bai sa ƙafarsa ba a yawon farauta a faɗin arewacin Najeriya dai kam,'' a cewar Abba.

Makusantanta sun ce sha'awarsa ga farauta ce ta hana yi shi yin karatu mai zurfi, "amma duk da haka yana da wayewa sosai ta zamani," in ji abokansa da dama.

Artabu da ɓarayi

Ali Kwara ya dade yana artabu da ɓarayi a ƙoƙarinsa na kama su.

Ya kan kama su a wasu lokutan ya miƙa su ga hukuma wasu lokutan kuma shi yake jagorantar sauya musu halaye sannan daga bisani a koya musu sana'o'i.

Musa Haruna wani aboki ne na kusa ga Alin wanda ya ce: "A da har wajen ajiye ɓarayi yake da shi a cikin gidansa. Da yawansu ya koya musu sana'ar fata wasu ma ya musu aure.

"Kuma duk wannan aiki yana yi ne da haɗin kan gwamnati da haɗin gwiwa da ita."

Wasu da dama ya kan yi amfani da su wajen saka su su tattaro masa ɓayanan sirri a kan wasu gaggan ɓarayin.

Sai dai danginsa sun ce duk da dai kullum shi yake samun nasara a kan ɓarayin, to hakan bai hana su yi masa barazana daban-daban ba a tsawon rayuwarsa.

"Ko a kwanakin baya kafin ya kwanta jinya sai da suka aiko masa wata barazanar cewa za su tare shi a hanya su sace shi, amma kamar ko yaushe Allah Ya kare shi," a cewar kanin nasa.

Faɗa da ɓauna

A shekarar 1999 ne Ali Ƙwara ya je farauta ya yi artabu da wata ɓauna a wani jeji da ke tsakanin garin Damban da Dagauda a hanyar Postikum.

A yayin da ɓaunar ta yo kansa sai ya rike kahonta tare da bai wa wani yaronsa umarnin harbinta.

"Bisa tsautsayi sai harbin ya samu cinyar Ali, amma duk da haka sai da ya ka da ɓaunar aka sake harbinta sannan ya yankata.

"Ya kwanta a wani asibiti a Kano Accord Surgery inda ya shafe tsawon wata biyar yana jinya har akai masa aiki a cinyar," a cewar Musa Haruna, wani da suka yi kuruciya tare da Alin.

Iyali

Ainihin uwargidan Ali kuma wacce ta kasance 'yar uwarsa Balarabiya kuma uwar 'ya'yansa Hajiya Ilham, ta rasu shekara tara da suka wuce.

A yanzu ya mutu ya bar wata macen ɗaya Hajiya Aymana. Sannan ya bar 'ya'ya hudu da suka hada da maza uku da mace ɗaya.

Sai jikoki huɗu, kuma an haifi jikarsa ta huɗun sa'a guda kacal bayan da Allah Ya karɓi rayuwarsa.