WTO: Buhari na yi wa Ngozi Okonjo-Iweala kamun kafar ƙasashen duniya

Buhari da Ngozi

Asalin hoton, State House

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fara yi wa Ngozi Okonjo-Iweala tsohuwar ministar kuɗin ƙasar kamun ƙafar shugabannin ƙasashen duniya domin ganin ta zama shugabar ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya.

Fadar shugaban na Najeriya ta ce, Buhari ya tattauna da shugaban majalisar Tarayyar Turai Charles Michel ta kafar bidiyo a intanet, wanda ya tabbatar da goyon bayan ƙasashen Turai ga Ngozi.

Sanawar da Femi Adesina mai magana da yawun shugaban ya fitar a ranar Juma'a ta ce shugaban yana jagorantar gwagwarmayar da Najeriya ke yi wa Okonjo-Iweala, tsohuwar Ministar Kudi ta kasar, domin zama baƙar fata kuma mace ta farko a matsayin shugabar WTO.

Sanarwar ta ce Buhari ya gode wa Tarayyar Turai kan goyon bayan da ta ba ƴar takarar ta Najeriya.

A ranar Laraba jakadun kasashe a ƙungiyar Kasuwanci ta Duniya WTO mai mambobi 164 suka gabatar da sunan Ngozi Okonjo-Iweala a matsayin sabuwar shugabar ƙungiyar.

Amma gwamnatin shugaban Amurka Trump na adawa da zaɓen Okonjo-Iweala, inda ta ke goyon bayan 'ƴar takara daga Koriya Ta Kudu Yoo Myung-hee.

Ma'aikatar harakokin wajen Najeriya ta ce, ƙasar za ta ci gaba da kamun ƙafar ƙasashe da masu ruwa da tsaki domin samun goyon bayansu ga Ngozi.

Akwai dai babban ƙalubale ga Najeriya wajen sauya ra'ayin Amurka wacce ke goyon bayan ƴar ƙasar Koriya ta Kudu.

Wakilan Amurka a ƙungiyar WTO sun fitar da sanarwa da ke bayyana goyon baya ga Yoo Myung-hee, tare da bayyana ta a matsayin wadda ta fi cacanta saboda ƙwarewarta a harkokin cinikayya.

Ƙungiyar WTO na fatan cimma matsaya kan zaɓin sabon shugaba. Kuma dole sai an samu jituwa kafin zaben sabon shugaban ƙungiyar.

Ƙasashe da dama ne suka yi gwagwarmayar ganin an naɗa Ngozi domin jagorantar muhimmiyar ƙungiyar kasuwanci ta duniya mai mambobi 164.

Babu tabbas kan abin da zai faru a ranar 9 ga Nuwamba da babban zauren ƙungiyar zai cimma matsaya kan naɗin wanda zai jagoranci ƙungiyar tsakanin tsohuwar ministar ƙundin Najeriya Ngozi Okonjo-Iweala da kuma tsohuwar ministar kasuwanci ta Koriya ta Kudu Yoo Myung-hee.