Shekarata 95 amma har yanzu ina amfani da shafukan sada zumunta - Tanko Yakasai
Ba kowa ne zai ga Malam Tanko Yakasai ba ya ce ya kai shekara 95 a duniya saboda Allah ya hore masa kyan ruwa.
Tanko Yakasai wanda aka haifa a 1925 ya ce "da waya nake duba labaran abubuwan da ke faruwa a duniya sannan kuma ina yin Whatsapp."
Da wuya a samu mai shekarun Malam Tanko Yakasai wanda ba ya amfani da gilashin ido, amma Malam Tanko ya ce shi kam gilashinsa ba ko yaushe ba.
"Da haka nake duba waya ba tare da gilashi ba. Ina da gilashin amma ba ya ƙaramin komai saboda haka ban cika amfani da shi ba."
Dangane kuma da batun lafiya, Tanko Yakasai ya ce babu wata cuta da ke damunsa duk da waɗannan shekaru masu yawa da yake da su, inda ya ƙara da cewa shi kam ya gaji tsawon kwana.
"Mahaifina ya rasu yana mai shekara 96 amma kakana ya mutu yana da shekara 105. Mahaifiyata ce ta mutu tana shekara 87. Haka Allah ya yi mu."
Malam Tanko Yakasai ya yi imani da maganar Bahaushe da ke cewa mai rabon ganin badi sai ya gani, ko ana muzuru da shaho.
Dattijon mai shekara 95 ya tuna baya dangane da irin wahalar da ya sha sakamakon gwagwarmayar siyasa.
"Ni a siyasata an ɗaure ni sau 10, ko dai a kama ni a kai ni gaban alƙali a ɗaure ko a tsare ni a ofishin 'yan sanda. Huɗu lokacin mulkin Turawa da kuma huɗu lokacin jamhuriyya ta Daya sannan biyu a zamanin mulkin soja wato lokacin Buhari da Babangida."











