Alpha Conde: Mai shekara 82 ya lashe zaben Guinea a wa’adi na uku

Shugaba Alpha Conde na Guinea

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Shugaba Alpha Conde na Guinea

Hukumar zaɓe a Guinea ta ce shugaban ƙasar Alpha Conde ya lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar ranar Lahadin da ta gabata.

Alƙalumman sakamakon zaɓen ya nuna Mista Conde mai shekara 82 ya samu kashi 59 na yawan ƙuri'u a zaɓen mai cike da ƙalubale.

Babban abokin hamayyarsa Cellou Dalein Diallo wanda ya yi ikirarin lashe zaɓen kafin sanar sakamako ya samu kashi 33 na yawan ƙuri'u.

Hakan na nufin Alpha Conde zai yi wa'adin mulki na uku.

Mr Diallo, 68, won 33.5% of the ballots, the electoral commission said.

"We are still going to refer the matter to the constitutional court, without having too many expectations," Mr Diallo told Agence France-Presse.

Sabon tsarin mulkin da masu zabe suka aminta da samar wa a watan Maris ya ba Shugaba Conde damar neman karin shekaru karagar mulkin kasar.

Sabon kundin tsarin mulki bai yi watsi da wa'adin shugabanci biyu ba, amma ya sake tsara matakin, don haka yawan wa'adin da aka yi a baya ba su cikin lissafi.

Mutane da dama ne aka kashe a watannin da aka shafe ana zanga-zanga bayan Mista Conde ya ayyana kudirinsa na neman wa'adin mulki na uku.

Babbar mai shigar da ƙara ta kotun hukunta laifukan yaki a duniya ICC, Fatou Bensouda, ta yi gargdin cewa waɗanda suka aikata laifi ko tunzura jama'a a rikicin zaben na Guinea za su fuskanci hukunci.

Fargabar ɓarkewar rikici

Rahotanni sun ce an girki jami'an tsaro da suka ƙunshi ƴan sanda da sojoji domin tabbatar da zaman lafiya bayan jin ƙarar harbe-harben bindiga a Conakry.

Ƴan sanda uku suka mutu a rikicin ya ɓarke ranar juma'a, kamar yadda kafofin yaɗa labaran Guinea suka ruwaito.

Kuma rahotannin sun ce an toshe Layukan sadarwa da na intanet.

Kamfanin dillacin labarai na Reuters ya ce an ji karar harbin bindiga a garin Sonfonia da ke kusa da Conakry inda mazauna yankin suka shaida wa Reuters cewa ƴan sanda sun tarwatsa masu zanga-zanga da harsashen roba.

2px presentational grey line

Abu biyar game da Guinea:

Map
  • Shugaban da ya jagoranci ƴancin kai Sekou Touré ya faɗawa Faransa a 1958 cewar: "Guinea ta fi son talauci cikin' yanci fiye da bautar bayi"
  • Jagoran gwagwarmayar "Black power"Stokely Carmichael ya dawo daga Amurka zuwa 1968, tare da matarsa Miriam Makeba, wanda ya zama babban ɗan gwagwarmaya a Afirka
  • Ita ce babbar mai arzikin dutsen bauxite - da ake samar da ƙarfen gorar ruwa
  • Gandun dajin Nimba, manyan gandun daji na hukumar Unesco da ke kan iyaka da Ivory Coast da Liberia, yana cikin manya a duniya
  • MawakiMory Kanté, sananne a wajajen 1980 musamman Yéké Yéké, ɗan asalin Guinea ne.
2px presentational grey line

Wanene Alpha Condé?

Guinea's President Alpha Condé

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mista Condé ya yi tazarce wa'adi na uku

Mr Condé toshon madugun adawa ne wanda a 2010 ya fara lashe zaɓen shugaban ƙasa, karon farko aka miƙa mulki ga farar hula.

Ya taɓa ɗaure shi kan ƙalubalantar Janar Lansan Conte, wanda ya yi mulki tsakanin 1984 zuwa mutuwarsa a 2008.

Wanene babban mai hamayya da Conde?

Cellou Dalein Diallo

Asalin hoton, AFP

Bayanan hoto, Mr Diallo ya yi fatan zai lashe zaɓen bayan karo uku yana takarar shugaban kasa

Cellou Dalein Diallo tsohon Firaminista shi ne babban mai hamayya da Conde.

Mista Conde ya doke shi a zaɓukan 2010 da 2015, ko da yake ya ce an tafka magudi a zaɓukan.

Bafulatani ƙabila mafi yawa a Guinea, amma kuma ƴan kabilar ta da ake kira Peul ba su taɓa shugabanci ba a Guinea saboda fuskantar wariya tun a zamanin mulkin shugaba Sékou Touré.

Tun da farko Mista Diallo da sauran manyan ƴan adawa sun yi barazanar ƙauracewa zaɓen kan zargin maguɗi.

Amma daga baya Mista Diallo ya ɓalle daga gamayyar ƴan adawa ya yanke shawarar takara a zaɓen.

Yanzu gamayyar ƴan adawa ta FNDC sun kira zanga-zanga a ranar Litinin