Matar da ke taimaka wa marasa lafiya a arewacin Najeriya

    • Marubuci, Umar Mikail
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Abuja Bureau
  • Lokacin karatu: Minti 3

Kamar yadda aka saba a kowanne lungu da saƙo na duniya, marasa lafiya kan shiga tashin hankali idan suka rasa mai agaza musu musamman idan suka kamu da cuta mai tsadar magani.

Marasa ƙarfi a arewacin Najeriya kuwa kan samu tallafi ne daga ƙungiyoyin agaji irinsu Creative Helping Needy Foundation (CHNF) ƙarƙashin shugabancin Fauziyya D. Sulaiman.

CHNF ta fara aiki shekara biyar da suka gabata a matsayin ƙungiya, kafin daga bisani ta samu rajista a matsayin gidauniya shekara biyu da suka wuce.

Babban aikin gidauniyar shi ne tallafa wa marasa lafiyara da ba su da kuɗin magani. Kazalika, marayu da iyayensu, yara da ba sa zuwa makaranta da makamantansu, su ma suna samun tallafi.

Ya zuwa yanzu, CHNF ta taimaka wa mutum fiye da 100 sannan kuma a kullum akwai marasa lafiya a kan layi da ke hanƙoron samun tallafi daga gareta.

Wace ce Fauziyya D. Sulaiman?

"Idan zan yi barci ko cin abinci sai na kashe wayoyina, idan ba haka ba marasa lafiya da masu bayar da tallafi za su yi ta kirana," in ji Fauziyya D. Sulaiman, a hirarta da BBC.

Hajiya Fauziyya uwar yara takwas ce - ciki har da tagwaye - kuma marubuciyar ƙagaggun labarai kuma labaran fim cikin harshen Hausa.

Ta yi aikin asibiti kafin daga bisani ta koma aiki da gidan talabijin na Arewa 24.

An haifi Fauziyya a shekarar 1981 a unguwar Fagge da ke Ƙaramar Hukumar Fagge a ƙwaryar birnin Kano.

Yadda gidauniyar CHNF ke samun kuɗi

Akasari kuɗin tallafin da CHNF ke tallafa wa mutane da su kan samu ne ta hanyar yayata buƙatun marasa lafiya a kafafen sada zumunta, a cewar shugabar ƙungiyar.

"Kashi kusan 99 cikin 100 muna samun su ne ta hanyar tallatawa a shafukan Facebook da WhatsApp da Twitter da Instagram.

"Akwai kuma ƙungiyar Uwar Gidan Shugaban Ƙasa Aisha Buhari ta Future Assured, wadda kan ba mu aikin tallafa wa mabuƙata. Mun taɓa tura wani marar lafiya da ta ɗauki nauyinsa na kusan naira miliyan 14."

Kazalika, ta ce akwai ɗaiɗaikun mutane da kan bayar da nasu tallafin idan sun ji muna nema wa marar lafiya agaji.

"Sarkin Kano Mai Murabus Muhammadu Sanusi II ya ɗauki nauyin marasa lafiyarmu sau biyu a baya. Shi ma Sarkin Kano na yanzu Aminu Ado Bayero ya ɗaukin maras lafiyarmu ta ƙarƙashin wata 'yarsa Aisha. Kwanan nan ma Baffa Babba Ɗanagundi ya biya kuɗin wata mai ciwon ƙafa.

"Shi ma Sarkin Musulmi Alhaji Sa'ad Abubakar ya taɓa ɗaukar nauyi. Ita ma 'yar gidan Gwamnan Kano Ganduje, Asiya ta ɗauki nauyin maras lafiya.

"Manya ba za su ƙirgu ba waɗanda muke da alaƙa da su. Amma akasari ba kai-tsaye suke mu'amala da mu ba, sai mun saka muna nema wa maras lafiya tallafi."

Haka ma, sukan samu tallafi daga wajen Najeriya da kuma ƙungiyoyin addinin Kirista.

"Mutanen da suke ba mu tallafi daga wajen Najeriya kusan ma sun fi ba mu tallafi - Hausawa da Larabawa.

"Larabawa suna ba mu tallafi sosai. Idan Hausawa suka ga muna neman tallafi sai su nuna wa iyayen gidansu Larabawa, su kuma su bugo waya. Akwai wadda ta taɓa ba mu miliyan ɗaya, wata ma miliyan biyu ta bayar aka saya wa wasu mutane gida.

"Ƙungiyar Kiristoci sun sha ba mu tallafi. Rabaran-Rabaran suna kira su ce ga tallafi amma mafi yawa sun fi ɗaukar nauyin maras lafiya."

'Yadda nake jagorantar ayyukan gidauniyar'

"Duk ranakun hutuna na ƙarshen mako ina waje, wani zubin ma tare da mai gidan muke fita ya kai ni wasu wuraren domin ya ba mu haɗin kai sosai," a cewar Fauziyya.

Ta ci gaba da cewa: "Akasari sai na tashi daga wurin aiki nake tafiya wurin aikin gidauniyar. Ina da wakilai a asibiti huɗu; Asibitin Malam Aminu Kano da Asibitin Ƙashi na Dala da Asibitin Nasarawa da Asibitin Sir Sanusi.

"In da na ji an fi samun matsala can nake tafiya, idan kuma babu matsala sai na tafi gida, sai da dare sai mu haɗu a lissafa kuɗaɗen da aka kashe da kuma abin da ake buƙata. Haka muke yi kullum domin kodayaushe muna da maras lafiya a asibiti."

Shugabar Gidauniyar Creative Helping Needy ta ce yanzu haka suna gina ofishi a kan titin Rimin Abzinawa da ke Ƙaramar Hukumar Gwale a Jihar Kano.