Abin da ya sa kasuwar zanen kwaikwayon halittu masu rai ke bunƙasa a Afirka

A cartoon by Nigerian animator Ridwan Moshood

Asalin hoton, RIDWAN MOSHOOD

Bayanan hoto, Ridwan Moshood ya ce yana kwashe sa'o'i da dama yana kallon bidiyon katun, yana koya
    • Marubuci, Daga Vivienne Nunis & Sarah Treanor
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Business reporters, BBC News

Dan Najeriya mai zanen kwaikwayon halittu masu rai Ridwan Moshood, ya sha alwashin koyon yadda ake zanen katun, shi ya sa ya kwashe sa'o'i da dama a shafukan intanet a Lagos, yana kallon darussan da ake koyarwa a YouTube kuma yana koya.

"Ina zuwa shagunan da ake shiga intanet, na kallo bidiyon yadda ake koyar da zane-zane sannan na rubuta abubuwan da na koya," in ji shi.

Yanzu, Moshood, mai shekara 26, yana cikin matasan da suka fi shahara a Afrika wurin zanen animeshin.

Shekaru biyu da suka wuce, kungiyar Cartoon Network Africa Creative Lab ta karrama shi saboda zanen animeshin da ya yi mai suna Garbage Boy and Trash Can.

Ya samu ilhamar yin wadannan zane-zanen ne daga irin abubuwa marasa dadi da ya fuskanta a makarantar sakandare, wadanda suka shafi shara da kuma cin zali a makaranta.

A still from the animated short Garbage Boy & Trash Can

Asalin hoton, RIDWAN MOSHOOD

Bayanan hoto, "Na kirkiri animeshin na Garbage Boy domin na nuna wa sauran mutanen da aka ci zali cewa abin da aka yi musu bai dace ba," a cewar Ridwan

"Garbage Boy tamkar rayuwata ce," in ji shi. "An ci zali na sannan aka rika zagina.

"Na yanke shawarar kirkirar animeshin din Garbage Boy domin ya zama wata hanya ta karfafa gwiwa da gafartawa. Sannan na nuna wa mutanen da aka ci zalinsu cewa abin da aka yi musu bai dace ba."

Tuni ya kafa kamfanin da ke kirkirar animeshin kuma yanzu yana sa ran kirkiro wani zanen katun wanda za a yi a Lagos, kuma a sanya masa suna In My Hood, kuma a rika wallafa shi a jere.

Koyi-da-kanka

Abin mamaki shi ne, yadda Ridwan Moshood ya koyi animeshin ba wani abu ne na daban ba.

"Mukan ji irin wadannan labarai a dukkan nahiyarmu," a cewar Nick Wilson, mutumin da ya kafa kungiyar zanen animeshin ta the founder of the African Animation Network, wadda ke birnin Johannesburg.

Mai zanen animeshin dan Najeriya Ridwan Moshood

Asalin hoton, RIDWAN MOSHOOD

Bayanan hoto, Ridwan Moshood yana fata sabon zane katun din da zai yi, wanda aka tsara Lagos, za a kaddamar da su a jere

Ya zayyana sunayen wasu kasashen Afrika inda masu basirar zanen animeshin suke tasowa: Najeriya, Ghana, Kenya, Uganda, Masar, Afirka ta Kudu, Mozambique da kuma Burkina Faso.

"Dukan inda muka je muka gano wanda ke da basirar animeshin, mukan gano suna da matukar hazaka kuma galibinsu suna koyarsa ne da kansu," a cewarsa.

Sai dai a yayin da labarin masu koyar da animeshin da kansu yake da karfafa gwiwa, akwai bukatar su rika samun horo daga wurin masana, in ji shi.

Doh D Daiga, wani dan kasar Kamaru ne da ke zanen animeshin wanda ke zaune a Burkina Faso. Shi ne yake kula da fannin horaswa da ci gaba a African Animation Network.

"Abubuwan da na koya a wannan harka sun nuna mani cewa akwai tarin matasa masu matukar basira wadanda ba a fito da irin hazakarsu ba" a cewarsa.

"Babban abin da ke yi wa Afrika tarnaki shi ne rashin samun horo."

A kwanan baya, an bayyana yin hadin gwiwa da wani kamfanin yin aimeshin na duniya Toonz Media Group da Baboon Animation. Kamfanonin biyu suna shirin gina makarantun zane-zanen animeshin a Afrika, baya ga wadanda ake da su.

Rawar da 'yan Afirka ke takawa

An saka wannan zanen animeshin din a cikin jerin wadanda za su iya cin gasa a bikin Annecy International Animation Film Festival

Asalin hoton, MY BETTER WORLD/CHRIS MORGAN

Bayanan hoto, An saka wannan zanen animeshin din a cikin jerin wadanda za su iya cin gasa a bikin Annecy International Animation Film Festival

Duk da rashin samun dama ta samun horo, ana yin zane-zanen kwaikwayon halittu masu rai.

Chris Morgan na kamfanin Fundi Films ya zana wasu animeshin kwankin baya wadanda ya yi wa lakabi da My Better World.

Yayi hakan ne domin jan hankalin yara 'yan makaranta a Afrika sannan ya karfafa gwiwar matasa masu irin wannan hazaka.

"Muna da masu yin irin wadannan animeshin fiye da 100 da ke aiki a kasashe bakwai kafin barkewar annobar korona," in ji shi, a tattaunawar da aka yi da shi daga Mpumalanga, Afrika Ta kudu.

An samar da matsakaitan fina-finai na animeshin 55 a harshen Ingilishi, Swahili, Hausa da kuma Somali.

Masu zanen animeshin kusan 100 ne suka kirkiri zanen My Better World a kasashe bakwai na Afirka

Asalin hoton, MY BETTER WORLD/CHRIS MORGAN

Bayanan hoto, Masu zanen animeshin kusan 100 ne suka kirkiri zanen My Better World a kasashe bakwai na Afirka

Yadda ake bayar da labarai masu wahala cikin sauki

Amma ba kowanne zanen animeshin ne ake yin sa domin matasan Afrika ba. Wata mai zanen na kwaikwayon halittu masu rai da ke Nairobi Ng'endo Mukii tana amfani da wannan dama wurin bayar da labarai masu wahala.

Fim dinta da ya fi shahara shi ne Yellow Fever, wanda aka tsara shi domin wayar da kai kan yadda matan Afrika suke yin bilicin.

"Na duba yadda mata ke yin amfani da maya-mayen bilicin a Kenya, da kuma abin da a ganimu shi ne kyawu," in ji ta, tana mai karawa da cewa tana so ta san "dalilin da ya sa hakan ke faruwa".

Wasu batutuwan da ta yi zanen animeshin a kai sun hada da gudun hijira da fasa-kaurin mutane.

Fim din Ng'endo Mukii mai suna film Yellow Fever ya yi bayani kan yadda matan Afirka ke yin amfani da mayukan bilicin

Asalin hoton, NG'ENDO MUKII

Bayanan hoto, Fim din Ng'endo Mukii mai suna Yellow Fever ya yi bayani kan yadda matan Afrika ke yin amfani da mayukan bilicin

Zane-zanen animeshin da ta yi sun sa ta samu lambobin yabo na kasashen duniya, ciki har da gasar zanen matsakaicin animeshin a bikin Chicago International Film Festival for Yellow Fever a 2013.

Cutar korona ta sa an samu karuwar masu son zanen animeshin

A yayin da masu zanen animeshin ke ci gaba da samun lambobin yabo na kasashen duniya, kamfanonin duniya na kara sanya ido a cikin harkar tasu.

A shekarar da ta wuce, Netflix ya sayi animeshin na farko da aka yi a Afrika, Mama K's Team 4 - wani katun ne da ke magana a kan wasu 'yan mata hudu da aka tsara shi a birnin Lusaka na kasar Zambia.

A lokaci guda, kamfanonin kasashen waje irin su Pixar suna daukar 'yan Afirka da ke zanen animeshin aiki.

Hasalima, kasuwar animeshin na kara bunkasa, a cewar Rob Salkowitz, wani dan jarida da ke daukar labarai kan fina-finan Amurka a mujallar Forbes.

"Ana samun karuwar bukatar animeshin a halin yanzu. Hakan na faruwa tun ma kafin barkewar annobar korona saboda shafukan da ke nuna fina-finai a intanet suna kishirwar sabbin zanen animeshin; zanen wani abu ne da masu kallo daga sassa daban-daban ke sha'awa," in ji shi.

Zanen animeshin da 'yar kasar Kenya Ng'endo Mukii ta yi

Asalin hoton, Ng'endo Mukii

Bayanan hoto, Zanen animeshin da 'yar kasar Kenya Ng'endo Mukii ta yi
Logo of the African Animation Network

Asalin hoton, AFRICAN ANIMATION NETWORK

2px presentational grey line